SOYAYYA: Budurwa ta bankawa kanta wuta saboda saurayi yaki biyan sadakinta a Zamfara

0

A jihar Zamfara ne wata budurwa mai suna Aisha Bello ta babbake kanta wuta saboda saurayinta mai suna Umar bai iya biyan kudin sadakinta.

Aisha wacce ke da shekaru 17 na zama ne a Albarkawa, karamar hukumar Gusau.

annan ta aikata wannan mummunar aiki ne saboda ta gaji da zaman kadaici.

Aminu Muhammed da abin ya faru a idon sa kuma mai unguwar kauyen Albarkawa ya shaida wa manema labarai cewa Allah yasa akwai mutane kusa da inda Aisha ta aikata wannan mummunar aiki sai suka yi maza-maza suka kawo mata dauki suka kashe wutar kafin ta sheka lahira.

Muhammed ya ce wannan abin takaicin ya faru ne bayan iyayen Aisha sun bukaci saurayinta Umar ya biya kudin sadakin Naira 17,000, shi kuma Umar ya ce bashi d wannan kudi.

” Aisha na jin haka kuwa sai ta sito galan din Fetur ta duldula wa kanta ta kyasta ashana. Sannan ko a daidai Aisha tana kokarin ta cinna wa kanta wuta kanwarta ta yi kokarin hana ta amma taki ji.

A yanzu haka Aisha na kwance a gida ana yi mata maganin gargajiya saboda mahaifinta bashi da kudin kauta asibiti.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Shehu Muhammed ya tabbatar da aukuwar wannan abin tashin hankali sannan kuma rundunar za ta ci gaba da yin bincike a kai.

Share.

game da Author