Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilan sa suka sa ya fi nada mata mukamin ministar kudi. Ya ce ya fi dora mace rikon harkokin kudade ne saboda iya kula da tattalin albarkatun kudaden da ba su wadata ba. Sannan kuma mace ta iya mako musamman a halin rashin wadatattun kudade.
Ya ce ya fi so mace ta rike Ma’aikatar Kudi saboda nan da nan a koyaushe a shirye suke wajen iya amfani da basirar su su yi amfani da abin da ake da shi ta inda ya dace a yi amfani da shi.
Buhari ya ce Allah ya albakarci kasar nan da kwararrun mata a kowane fanni daban-daban, na cikin gida da kuma kasa-da-kasa.
Ya yi wadannan jawabai ne jiya Alhamis a lokacin da ya karbi Shugabannin Mata na Jam’iyyar APC, shiyyar FCT, Abuja karkashin Hajiya Salamatu Baiwa.
“Ina farin cikin ganin yadda na ke bai wa mata rikon amanar harkokin kudin kasar nan. Shugaban Jam’iyya shaida ne a kan haka.
“Mata ta kowane fanni sun iya tattali, ko a gida idan aka yi la’akari da yadda suke ririta kudin cefane, za a tabbatar da haka.”
Daga nan sai ya kara da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bai wa mata muhimmanci wajen ba su mukaman kawo ci gaba a kasa. Ya ce ya gamsu kwarai da irin rawar da mata ke takawa a dukkan mukaman kasar nan.
Ya ce zai shigar da mata sosai wajen kokarin inganta kanana da matsakaitan masana’antu a kasar nan a wannan zango na biyu.
Sannan kuma a harkokin noma zai shigar da mata da matasa su ma sosai kamar a cikin inganta kananan masana’antun.
Da ya karkata kan batun noma kuwa, Buhari ya ce, “Na san babu wani maji karfin da ya koma harkar noma shekaru uku baya zuwa yau, kuma a ce ya na kukan tabka asara.”
A na ta jawabin, shugabar matan ta taya Buhari murnar nasarar da ya samu a kan PDP da abokin takarar sa, Atiku Abubakar, a Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa.