Mun shirya yi wa Atiku da PDP jina-jina a Kotun Koli – Oshiomhole

0

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, ya jaddada cewa APC za ta yi wa PDP da dan takarar ta, Atiku Abubakar jina-jina a Kotun Koli.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada cikakken labari a ranar Laraba, yadda Buhari ya kayar da Atiku a Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa a karkashin alkalai biyar.

Jim kadan bayan kammala shari’ar, Atiku ya ce hukuncin cin fuska ne da rashin adalci, don haka zai garzaya Kotun Koli.

Yayin da Oshiomhole ya kammala ganawa da Shugaba Buhari a jiya Laraba, ya bayyana cewa APC ta yi shiri tsaf domin sake kayar da PDP da Atiku a Kotun Koli.

“Matsawar da dokar Najeriya za a yi hukunci, to ko ma Kotun Duniya Atiku da PDP za su je, sai su yi ta tafiya. Ba mu damu ba, mun san bata lokaci za su yi, ba nasara za au yi ba.

” Saboda Dokar Najeriya dai ba ta PDP ko APC ba ce. Ita hujjar da aka gabatar mata za ta yi amfani da shi. Wato Kotun Koli za ta sake nazarin burbudin tarkacen abin da su Atiku suka gabatar a Kotun Daukaka Kara a matsayin hujja ne, ba wani sabon abu za a sake kawowa ba.

“Idan aka dubi yadda alkalan Kotun Daukaka Kara suka rika yin biji-biji da hujjojin da PDP da Atiku suka gabatar, to ko wanda ma bai san shari’a ba ya san ba su da wata madogara kawai.

“An yi kokawa sau biyu, kuma duk sun sha kaye. Idan za su hakura su hakura, su bi sahu a yi tafiyar ciyar da Najeriya gaba tare da su.

” Shugaba Muhammadu Buhari a shirye ya ke ya sake kafsawa da Atiku a Kotun Koli. APC ta shirya sake kokawa da PDP a Kotun Koli. Haka ni ma Oshiomhole na sake shirya kokawa da dan uwama, Uche Secondus, Shugaban PDP a Kotun Koli.”

Share.

game da Author