Sanata Dino Melaye ya ki amincewa da nadin da jam’iyyar PDP ta yi masa na zama darektan kamfen din jam’iyyar a zaben gwamnan jihar Kogi dake tafe.
Dino ya ce ba zai yi wannan aiki ba jam’iyyar ta nada wani kawai. Daga nan sai yayi wa jam’iyyar fatan alkhairi a zaben da za a yi a Nuwamba.
Haka Dino ya rubuta a shafinsa na Tiwita.
Idan ba a manta ba Sanata Dino Melaye ne ya zo na hudu a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka yi a jihar Kogi.
Kanin tsohon gwannan jihar, Musa Wada ne ya lashe zaben da kuriun daliget sama da 730, inda mai bi masa ya samu kuri’u 710.
Sanata Dino ya samu kuri’u 70 ne kacal a zaben.
Bayan haka ne jam’iyyar a Abuja ta nada shi darektan kamfen din Musa Wada da ya lashe zaben, amma kuma tuni ya ce ba zai karbi wannan aiki ba.