Za a yi wa malamai jarabawar kwarewa a jihar Yobe

0

Gwamnan jihar Yobe Mai-Mala Buni ya bayyana cewa gwamnati za ta yi wa malaman makarantun gwamnati jarabawar kwarewa a jihar.

Buni ya sanar da haka ne a wata takarda da kakakinsa Abdullahi Bego ya raba wa manema labarai ranar Laraba.

A takardar Buni ya yi bayanin cewa gwamnati za ta yi haka ne domin inganta fannin ilimin jihar bisa ga shawarwarin da kwamitin zartaswa ta bada.

Idan ba a manta ba a watan Yuli ne gwamnan jihar ya kafa dokar ta baci a fannin ilimin jihar ganin cewa dalibai basu samun ilimin boko na gari a jihar.

Bayan haka ne gwamna Buni ya kafa kwamiti domin zakulo hanyoyin da za abi wajen gyara fannin ilimi a jihar.

Ga shawarar da kwamitin ta ba da

1. Gudanar da jarabawar kwarewa ga duk malaman makarantun jihar.

2. Tantance takardun malaman.

3. Zakulo malaman dake bukatan horo da kara wa wadannan suka cancanci karin girma ko kuma canjin wurin aiki.

4. Daukan karin kwararrun malamai.

5. Gina makarantu irin na zamani domin koyar da darussan kimiya, fasaha da lissafi a mazabu uku dake jihar.

Bayan haka Buni ya bayyana cewa gwamnati ta zabi wasu makarantun sakandare na gwamnati domin maida su makarantun zamani a jihar.

Wadannan zababbun makarantu kuwa sun hada da makarantar sakandare dake Damaturu, kwalejin koyar da kimiya da fasaha dake Potiskum da kwalejin koyar da kimiya da fasaha dake Nguru.

A karshe Buni ya ce gwamnati za ta tabbata wannan shawarwari da aka bata sun tabbata domin inganta makarantun jihar.

Share.

game da Author