TITIN KADUNA-ABUJA: Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da matafiya

0

Kwanaki na biyu kenan a jere ana yin garkuwa da mutane a titin Abuja-Kaduna kuma har yanzu ba a kama koda mutum daya ba.

Daily Trust ya ruwaito yadda aka yi garkuwa da wasu matafiya masu dimbin yawa a hanyar ranar Litini da safe. Kamar yadda aka ruwaito, wani da Allah ya sa ya tsira daga wannan hari ya bayyana cewa maharan sun kashe mutane uku a wannan hari sannan sun tafi da mutane da dama cikin kungurmin daji.

” Nima dai Allah ne ya kubutar dani amma na kirga gawa 3 da aka kashe sannan masu garkuwan sun arce da wasu da dama cikin daji.

A wani rahoton kuma, a ranar labaraba ma maharan sun tare hanyar da misalin karfe 9 na safe. Inda suka arce da wasu mutane harda daliban jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya a hanyarsu na zuwa Kaduna daga Abuja.

Punch ya ruwaito cewa jami’ar ta tabbatar da bacewar daliban ta uku da ke matakin karshe a jami’ar.

Bayan haka kuma an gani a wani Bidiyo da ya karde shafukan sada zumunta a yanar gizo inda tawagar tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Dan-kwambo ya fadawa wadannan masu garkuwa, sannan a bidiyon an nuna wata mata matafiya tana rokon su taimaka su dauke su su wuce da su.

Wannan sabon hare-hare ya tada wa matafiya hankali matuka musamman yanzu da ake ganin abu yayi sauki kuma sai gashi abu ya dawo gadan-gadan a cikin ‘yan kwanakinnan. ” Tun daga ranar Litini ake yin garkuwa da mutane a wannan hanya batare da an kamo masu yi ba.” Inji wani direban mota.

Share.

game da Author