Hukumar kula da saida man fetur (DPR) ta bayyana cewa ta fara zagayen dudduba gidajen man dake jihohin Sokoto da Kebbi domin bankado gidajen man dake siyar da mai ba bisa ka’ida ba.
Babban jami’in hukumar dake kula da shiyyar Sokoto, Muhammed Makera ya sanar da haka da yake ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Sokoto ranar Laraba.
Makera yace DPR ta fara wannan aiki ne domin gano masu siyar da mai ba bisa ka’ida ba da kuma gano gidajen man dake aiki ba tare da sun mallaki lasisi.
“ A cikin gidajen mai 11 da muka garzaya mun gano guda uku da suke yin zamba a wajen saida man su da kuma yin aiki ba tare da lasisi ba.
Makera ya ce hukumar za ta ci gaba dayin irin wannan bincike kuma yayi kira ga mutane su rika tona asirin gidajen man da ke zaluntar mutane ta hanyar yin ha’inci a wajen saida mai.
Makera ya kuma shaida cewa duk gidan man da hukumar ta rufe za ta biya taran Naira 100,000 kafin a bude gidan man.
Ya ce ya yi mamaki yadda mafi yawan gidajen man da suka lelleka ke nuna su basu da masaniya game da irin ka’idojin hukumar.
“Ina kira ga mutane da su rikaajiye wayoyin su idan suka shiga gidajen mai sannan masu shan taba su rika hakuri idan suka shiga gidajen mai.