Wannan labari ya yi daidai da wata karin magana da ake cewa, ‘ana bikin duniya ake na kiyama.’ A yayin da ‘yan Najeriya ke zaman makokin bindige wani kanar da wasu sojoji biyar da Boko Haram suka yi a tsakiyar watan Yuli, shi kuma Kwamandan Yaki da Boko Haram na can na ragabzar shirya dabdala ana shagali.
Baya ga makoki da iyalai da ‘yan Najeriya ke yi na rasa zaratan sojojin, a na ta bangaren ita kuma hukumar tsaro ta sojoji har sassauta tutar ta domin jimami da nuna rashin jin dadin abin da ya faru na kisan sojojin da Boko Haram suka yi.
Ana cikin wannan yanayi ne shi kuma Babban Kwamandan Runduna ta 7 da ke Maiduguri, Bulama Biu ya samu karin girma ko karin igiya zuwa Manjo Janar a ranar 9 Ga Yuli.
Mako guda bayan wannan karin girma ne Biu ya aika wa Boko Haram sako ta kafafen yada labarai cewa su zubar da makamai su “taya shi murna, ko kuma ya yi musu kakkabar-‘ya’yan-kadanya.
Ya yi wannan kakkausan sakon ne a ranar 17 Ga Yuli, 2019.
Sai dai kuma wajen karfe 6 na yamma a ranar da Manjo Janar Biu ya yi wa Boko Haram kurari ne aka bindige sojojin shida a wani farmaki da aka kai wa sojojin Najeriya, kilomita 50 daga Maiduguri, a wani kauye da ake kira Jakana.
Dama Boko Haram sun taba kafa sansanin su a Jakana, karamin gari da ke kan titin Maiduguri zuwa Damaturu.
Kafin a kashe sojojin shida ciki har da kanar din, sai da aka yi gumurzu sosai, saboda farmakin bazata ne maharan suka kai wa sansanin sojojin.
Sannan kuma wasu sojoji sama da dozin biyu da suka ji raunuka, aka garzaya da su asibitin sojoji da ke Maiduguri.
Duk wannan barna da asara da aka yi wa sojoji da Najeriya, ba su hana Manjo Janar Biu tara manya masu kumbar susa a yi ragabzar dabdalar murnar karin girma da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi masa ba.
Daga cikin manyan ‘yan siyasar da ya gayyata suka halarta, har da Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum.
PREMIUM TIMES ta samu kwafe-kwafen katin dabdalar shagalin da kuma hoton Biu zaune tare da Babagana Zulum.
PREMIUM TIMES ta tura wa Manjo Janar Biu sakon tambayar neman jin dadilin shirya dabdalar da ya yi a lokacin da ake jimamin rashin Kanar na soja sukutum da kuma wasu hafsoshi biyar. Sai dai bai maido amsa ba, har lokacin da aka buga wannan labari.
Su ma Kakakin Hedikwatar Tsaron Soja, Onyema Nwachukwu da Kakakin Sojojin Najeriya, Sagir Musa, ba su amsa tambayoyin da PREMIUM TIMES ta yi musu dangane da wannan dabdala ba.
Biu yabi son rai – Charles Omole
Wani mai sharhi a kan al’amurran tsaro mai suna Charles Omole, ya ce dabdala da walimar da Biu ya shirya a daidai lokacin da ake makokin rashin jami’an sojoji shida, zai iya darsasa kashe karfin guiwar yaki da Boko Haram.
“A baya an dade ana tafiya a matsayin tsari na ‘yan uwantaka tsakanin manyan hafsoshin sojoji da kananan su har zuwa karabiti. Amma daga shekaru bakwai da suka shude har zuwa yau, ana kara samu tazara sosai tsakanin manjan jami’an sojoji da na ‘yan su tsakanin su da manyan da sauran kanana karabiti.” Inji Omole.
Sai dai kuma Omole ya ce mai yiwuwa Biu ya yi abin nan da Hausawa ke cewa, “da na gaba ake gwada zurfin ruwa.” Domin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Shugaba Muhammadu Buhari duk sun halarci walimar dabdala a lokacin da ake jimamin wani gagarimin rashi ko barna da ta afku a kasar nan.
Sai dai kuma wani mai sharhin kan al’amurran tsaro mai suna Ona Ekhomo, ya ce Biu bai yi rashin kyautawa ba sosai. Amma dai duk da haka, “kamata ya yi a ce ya dage ranar da shirya dabdala zuwa wata rana can gaba daban.” Inji shi.