Wani kungiya mai zaman kansa mai suna ‘Malaria Consortium’ zai fara raba maganin zazzabin cizon sauro mai suna ‘Sessional Malaria Chemoprevention (SMC)’ domin kare yara ‘yan kasa da shekara biyar daga kamuwa da cutar a Najeriya.
An sarrafa SMC ne domin samar da kariya wa yara kanana daga kamuwa da zazzabin cizon sauro a lokacin damina.
A takarda da kungiyar ya mika wa PREMIUM TIMES kungiyar ya bayyana cewa za a fara rabon wannan magani ne a wasu kasashen Afrika guda uku.
Wadannan kasashe sun hada da Najeriya, Bukina Faso da Chadi.
kamar yadda yake a bayyane karara daga bakin kungiyar, zai dauke ta tsawon watanni har hudu daga watan Yuli zuwa Oktoba domin yin aikin rabo wannan magani a kasashen.
“Bayan gudanar da bincike da aka yi sakamakon ne ya sa muka zabo kasashe 11 a Afrika da Kudu maso gabashin Asia da za mu tallafa wa da wannan magani sannan daga cikin wadannan kasashe mun zabi Najeriya, Bukina Faso da Chadi a matsayin kasashen da ya kamata a fara da su ganin cewa sune kasashen duniyan da zazzabin cizon sauro ya fi ya wa ta’adi matuka.
Jami’ar kungiyar, Rassi ta ce sun kammala shiri tsaf domin fara rabon wannan magani a Najeriya.
Ta kuma ce kungiyar zai hada hannu da duk sassan gwamnati, ma’aikatan kiwon lafiya, sarakunan gargajiyya domin samun nasara a wannan aiki da ta sa a gaba.
Kungiyar Malaria Consortium ya hada hannu da hukumomin samar da tallfi na USAID, UKaid domin ganin an fatattaki zazzabi kwata-kwata a kasarnan.
Kungiyar ya fara aiki a kasashen kudu da Saharan Afrika ne tun a shekarar 2013.
Sakamakon binciken da wasu likitoci daga kasar Britaniya da Thailand suka yi a kwanakin baya ya nuna cewa zazzabin cizon Sauron da baya jin magani ya bullo a kasashen Asia da Afrika.
Sakamakon binciken ya nuna cewa magungunan ‘Artemisinin da Piperaquine’ da ake amfani da su wajen maganin zazzabin basu aiki a jikin mutane.
Roberto Amato ma’aikacin ‘Wellcome Sanger Institute’ dake kasar Britaniya ya bayyana cewa cutar na yaduwa kamar wutan daji sannan yana da wahala a samu sauki idan aka kamu.