ZABEN GWAMNA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar PDP ta yi amfani da binciken kwakwaf a takardun zabe

0

Kotun Daukaka kara ta ce jam’iyyar PDP da dan takaran gwamnanta a zaben 2019, Isa Ashiru sun yi latti wajen neman a basu daman yin amfani da masu binciken kwakwaf wajen duba takardun daka shigar da alkaluman sakamakon zaben gwamnan jihar.

Tun a kotun sauraren kararrakin zabe na jihar ta yi watsi da wannan dama da PDP ta nema.

Alkalin kotun ya bayyana cewa PDP da dan takaranta basu shigar da wannan kuka nasu cikin lokacin da aka kayyade domin mika ire-iren wadannan korafe-korafe.

A dalilin haka tuni tun a baya kotun sauraren kararrakin zabe a Kaduna ta bayyana cewa PDP ba yi abinda ya kamata tayi ba da wuri.

Bayan yanke wannan hukunci sai PDP ta garzaya kotun daukaka kara domin kalubalantar wannan hukunci na Kotun Kaduna.

Mai shari’a M. A. A Adumein da ya ke bayyana hukuncin kotu ya ce lallai itama kotun daukaka kara tabi sahun kotun sauraren kararrakin zabe wajen yin watsi da wannan dama da PDP ta nema.

Lauyoyin gwamna Nasir El-Rufai da na Jam’iyyar APC duk sun roki kotu tun a baya ta yi watsi da wannan kara da dama da PDP ke so ayi mata na a yi binciken kwakwaf.

Share.

game da Author