Yadda Fulani suka gwangwaje shagulgulan Sallah a Gusau

0

A yau ne har zuwa yammacin wannan rana ake ci gaba da shagulgulan bukin Sallah a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Bukin dai kusan fuska uku gare shi. Na farko dai ana kallon sa da fuskar murnar wanzuwar zaman lafiya a jihar, tun bayan saukin hare-hare da garkuwa da kashe-kashen da aka samu tun bayan hawan gwamna Bello Matawalle.

Na biyu kuma buki ne ya zo daidai a lokacin Sallah Babba. Kenan tilas ya zama ranar farin ciki ga al’ummar jihar da kasa baki daya.
Dalili, hakan ya kara tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a jihar, sai dai addu’ar Allah ya sa hakan ya dore.

Na uku kuma, wannan shagali ya sa Fulani makiyaya sun samu dama da ‘yancin shiga duk inda suka ga dama a jihar.

Gwamna Matawalle ne da kan sa ya gayyaci Fulani domin su shigo Gusau a yi rubdugun shagulgulan wasan Sallah.

Ya gayyato su su yi wasan sharo, wato shadi domin hakan ya sake dawo da kyakkyawan zumunci da kuma zamantakewar juna a jihar, wadda ta shafe shekaru takwas ba tare da zaman lafiya ba.

A yau Talata an yi gagarimin gangamin Fulani da sauran al’ummar jihar aka rika gudanar da shagulgula a gaban Gwamna Matawalle, a Filin Bajekoli na Gusau.

Matawalle shi kan sa da wasu makarraban sa, duk shigar Fulani suka yi.

Tun bayan hawan sa mulki a cikin watanni biyu kacal, Matawalle ya samar da zaman lafiya bakin gwargwado.

Kokarin sulhunta Fulani makiyaya da ‘yan banga da ya yi, ya samar da zaman lafiya bayan tarukan da aka rika gudanarwa har da jami’an tsaro da gwamna da kuma wakilan ‘yan bindiga.

Ya zuwa karshen Yuli dai ‘yan bindiga sun sako mutane kimanin 300. Haka rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta saki wasu Fulani da ake tsare da su kusan 100.

Wani mazaunin Gusau mai suna Aliyu, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa tabbas zai iya cewa zaman lafiya ya fara samuwa a Gusau.

“Dangi na da ke kauye sun koma gidajen su. Kuma wani kawu na da ya daina zuwa gona da dadewa, a yanzu ya na tafiya mai nisan gaske ya je gona. A da kuwa ko kyautar milyoyin kudade za a ba shi, bai isa ya shiga cikin dajin ya ce zai dangana da gonar sa ba.”

Shi kuwa Alhaji Ibrahim, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa, “Tun da rana wajen 12 na fara ganin abin mamaki da farin ciki a cikin Gusau. Fitowa na yi kofar gida, na rika ganin yara matasa Fulani daga kauyuka su na ta tururuwar shigowa cikin Gusau, kowane dauke da sanda.

“Ni ban zabi PDP ba, kuma ban zabi Gwamna Matawalle ba. Amma a gaskiya zan iya ce maka na yi murna da PDP ta samu nasara a Jihar Zamfara.”

Wata kwakkwarar majiya a Gusau, ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa kafin wannan gangamin sharo da gwamna ya gayyaci Fulani makiyaya a Gusau, wasu malamai sun same shi suka nuna masa rashin gamsuwar su da taron shagalin da ke gudana a yau.

Sai dai kuma da yake manufar gwamnan Matawalle shine hada kan mutanen jihar bai saurari wani suka da ake kokarin yi wa wannan buki ba.

An shirya wannan buki ne domin hada kan mutanen jihar da suka dade suna fama da hare-hare da taddanci da garkuwa da mutane. Jama’a sun amsa kiran gwamnan Matawalle kuma ya sha ambaliyar yabo da jinjina daga mutane kasarnan ba Zamfara ba kawai.


Share.

game da Author