Yadda Albasa ke tsaida Habo da wasu amfanin sa 10

0

Albasa yan da matukar amfani a jikin mutum, ba wajen gyara abinci ba kawai har da gyara lafiyar mutum.

Ga amfanin Albasa

1. Yana tsayar habo – Idan aka dora barin albasa a kasan hanci, zafin sa jini ya tsaya cak.sa habo zai tsaya.

2. Yana dauke da sinadarin ‘Vitamin C – Sinadarin ‘Vitamin C na kawar da mura, tari, warkar da ciwo sannan yana kara kyan fata da tsawon gashi.

3. Yana dauke da sinadarin ‘Chromium’ wanda ke kare mutum daga kamuwa da ciwon siga.

4. Akwai sinadarin ‘Quercetin’ wanda ke hana kamuwa da cutar daji musamman dajin dake kama fata, ciki da dubura.

5. Yana rage kiba a jiki.

6. Akwai sinadarin ‘Folate’ a albasa wanda kan taimaka wa mutum wajen yin barci da hana gajiya.

7. Albasa na kare mutum daga kamuwa da cutar sanyi dake kama al’auran maza da mata.

8. Yana kare mutum daga kamuwa da hawan jini, cututtukan dake kama zuciya kare.

9. Yana kara gashi da tsawo.

10. Albasa na taimakawa wajen saurin nika abinci a ciki.

Share.

game da Author