WATA SABUWA: Kungiyar Shiite ta karyata datakar da zanga-zanga da jami’in ta ya sanar

0

Kungiyar IMN da aka fi sani da Shiite ta karyata babban darektan yada labaran ta Ibrahim Musa da ya fitar da sanarwar cewa Kungiyar ta dakatar da ci gaba da zanga-zanga da take yi na beman a saki shugabanta Ibrahim Elzakzaky dake tsare.

Kungiyar tace ba da yawun ta Ibrahim ya fitar da wannan takarda ba.

Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne aka rika yada wa cewa kungiyar ta dakatar da ci gaba da zanga-zanga da ta ke yi.

Sai dai kuma a ranar Juma’a sai kuma kungiyar ta musanta wannan magana.

” Ba da yawun mu bane Ibrahim Musa ya fidda wannan takarda. Ya yi gaban kansa ne kawai. Domin mu a tsarin mu babu wanda zai yanke hukunci kan koma menene sai gaba daya an hadu an amince da shi. Shi ko gaban gan sa yayi.
Haka kawai wani ba zai yi gaban kansa ba don ya samu dama.

” Saboda haka muna so mu tabbatar muku da cewa muna nan a kan bakan mu na sai fa gwamnati ta saki shugabanmu Ibrahim Elzakzaky. Zamu ci gaba da gudanar da zanga-zanga har sai anyi abin da muke so.

” Sannan kuma maganar Kotu bai isa ya haramta kungiyar mu ba har sai an samu amincewar majalisa. Wannan ne kawai zai tabbatar da haramcin kungiyar mu.Saboda haka babu gudu babu ja da baya muna nan daram kan abinda muka sa a gaba. Za muci gaba da zanga-zanga har sai an saki shugaban mu komai daren dadewa.

Share.

game da Author