Masu zanga-zanga sun nemi ‘Amnesty International’ ta fice daga Najeriya

0

PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayani daga jami’an Kungiyar Amnesty International cewa masu zanga-zangar sun yi dafifi a kofar shiga ginin ofishin na ta a yau Juma’a.

Sun kuma nemi jami’an kungiyar ta Jinkai ta Duniya da su fice daga Najeriya.

Kakakin Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu zanga-zangar sun a goyon bayan gwamnatin tarayya ne, kuma sun rika nuna fushin su a kan yadda AI din ta ke sukar gwamnatin Buhari.

Sun isa bakin kofar shiga harabar ginin dauke da kwalaye da kyallayen da aka yi wa rubutu masu nuna kakkausar suka ga Kungiyar Jinkai, wato Amnesty International.

Sanusi ya kara da cewa sun kuma rika rera wakoki na batunci ga kungiyar ta ‘Amnesty International.’

Wannan zanga-zanga ta zo ne bayan da aka rika watsa ji-ta-ji-ta a soshiyal midiya cewa gwamnati na shirin bayyana AI a matsayin kungiya mai barazana ga tsaron kasa.

An yi zargin ta na goyon bayan wani gagarimar zanga-zangar game-gari ta kasa baki daya da ake shirin yi a kasar nan.

A zaman yanzu dai wasu dandazon jama’a masu rajin sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da suka sa wa gangamin su suna ‘RevolutionNow’, su na shirin gudanar da zanga-zanga ta game-gari a ranar 5 Ga Agusta a cikin birane 21 na fadin kasar nan.

Su na shirya zanga-zangar ne a karkashin dan taratsi kuma mawallafin jaridar soshiyal midiya ta Shahara Reporters.

Ba wannan ne karon farko da aka taba yi wa Amnesty International zanga-zanga a Abuja ba.

PREMIUM TIMES ta taba buga yadda aka taba daukar sojojin hayar matasa aka biya su ladar kudade suka yi wa kungiyar ta agaji zanga-zanga watannin baya da suka gabata.

Idan ba a manta ba, Sowore ya kasance mai adawa da gwamnatin Goodluck Jonathan kafin zaben 2015.

Bayan Buhari ya ci zabe, shi da jaridar sa Sahara Reporters sun koma sun a sukar gwamnatin bayan da ya ga cewar Buhari ya kauce daga akidar da aka san shi, kamar yadda ya bayyana.

A karshe shi ma ya fito takarar shugabancin kasar nan a zaben 2019.

Share.

game da Author