Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Mohammed Shehu ya bayyana cewa mahara da dama sun ajiye makamai sun rungumi zaman lafiya a jihar.
Shehu ya bayyana cewa tun bayan shirin yin sulhu a tsakanin mazauna mahara, Fulani da manoma da gwamna Bello Matawalle ya kirkiro mahara da dama ne suka yi na’am da shirin.
Ya kara da cewa tuni har wasu daga cikin maharan ne ke fada da wadanda suma ki mika makamasu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Nagogo ya shaida wa gwamna Matawalle a fadar gwamnatin jihar a Gusau cewa mahara da dama sun karbi shirin sulhu din hannu bibbiyu.
Bayan nan ya nuna wa gwamna wasu daga cikin manyan bindigogi, harsasai, katan sojoji da mahara suka mika wa ‘yan sanda.
A jawabinsa, gwamna Matawalle ya roki maharan da su karbi wannan shiri na sulhu su mika makaman su domin samun zaman lafiya a jihar.