Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum,
Ya ku ‘yan uwana masu girma, masu daraja, masu albarka! Ina mika sakon gaisuwar ban girma zuwa ga re ku baki daya, tare da fatan wannan sako nawa zai riske ku cikin koshin lafiya da annashuwa. Allah yasa hakan, amin.
Ya ku jama’ah! Lallai ku sani, hakika shi goyon bayan gaskiya da masu gaskiya da tsayawa akan gaskiya da fadin gaskiya da aikata gaskiya cikin mu’amala da magana da sauran al’amurran rayuwa Ibada ne, kuma cikar kamala ne, nagarta ne, kuma riko ne da addini, domin yin hakan umurni ne na Mahaliccin mu.
Lallai duk mutumin da ya riki gaskiya to da wuya ace yau gaskiyar sa ta kare, domin Allah yana tare da masu gaskiya, kuma yayi alkawarin kasancewa tare da su a koda yaushe, da kuma dora su akan makiyan su!
Lallai duk wanda ya dage wurin ya jiyar da al’ummah gaskiya komai dacinta, to lallai za su godewa dandanon zakin ta a karshe, ko da ya hadu da wahalhalu a farkon al’amari.

Ya ku ‘yan uwa na masu daraja! Don Allah ku dubi yadda rashin gaskiya ya bata muna kusan dukkanin mu’amalolin mu; cikin masu mulkin mu, cikin talakawa, cikin addinin mu, cikin malaman mu, cikin kasuwanci mu, cikin zaman auren mu, cikin sana’oin mu da sauran al’amurran mu na rayuwa gaba daya.
Hakika a duk inda ka samu mai fadin gaskiya tsakanin sa da Allah, da tsayawa akan maganar sa, zaka samu wasu mutane da basa son gaskiyar sun sa shi a gaba da tsangwama, batanci, cin mutunci, da kokarin ganin bayan sa da kokarin tozarta shi. Amma a daya gefen kuma, zaka samu rayuwar sa da ban sha’awa, ga samun sauki da taimakon Allah, kuma zai samu shaida mai kyau na yabawar jama’ah masu nagarta.
Ya ku ‘yan uwa na masu daraja! A daya gefen, ya kamata mu tambayi kawunan mu, shin wai menene ribar karya ne? Dukkanin mu dai muna sane da cewa ita karya wallahi tana jawo wa mai yin ta mai goyon bayan ta kaskanci, wulakanci, gamuwa da fushin Allah, cin Karo da munanan matsalolin rayuwa, kuma daga karshe ba za’a taba cin nasara da karya ba har abada.
Ku sani! Wanda duk ya lizimci goyon bayan karya da makaryata, don dan abun duniyar da yake samu, kuma ya kasance mai yawan karya a maganar sa, da sauran ayyukan sa, to lallai wannan mutum ya tabe, kuma yayi babbar hasara, sannan ba zai gushe ba har karya ta kai shi aukawa cikin wutar Jahannamah.
Lallai ko shakka babu, har kullun, Allah yana tare da bayin sa masu gaskiya a cikin dukkan rayuwar su.
Don Allah, ina rokon iyaye da malamai masu tarbiyya da dukkanin jama’ah, da a kula da kai wurin nisantar karya, kuma a lura da yara, kada su tashi da yawan karya, da koyon karya a cikin maganar su ko mu’amalar su, ko su zamanto masu goyon bayan karya da makaryata.
Mu sani! Goyon bayan gaskiya komai dacinta, ko za’a zage ka akan ta ne, da goyon bayan masu gaskiya ko da kai kadai ne, Ibada ce, kamala ce, siffah ce ta bayin Allah na kwarai!
Allah yasa mu dace, yayi muna jagora, amin.
Ya ku jama’ah masoya gaskiya! Wallahi, ku sani, muna goyon bayan Sarkin Kano ne Malam Muhammadu Sanusi II, ba domin wani abu ba, face sai don gaskiyar sa, rikon amanar sa, son talakawan sa, son ci gaban al’ummar sa, fadin gaskiyar sa, kokarin kawo gyara da ci gaba da canji mai nagarta a cikin al’ummar sa da sauran halaye na kwarai na gari, masu yawan da wannan wuri ba zai isa duk mu kawo su ba. Wallahi wanda duk yasan Mai Martaba Sarki to zai yi shaida a kan hakan. Sannan kuma daga cikin dalilan mu na kokarin kare martabar Mai Martaba Sarki, kasancewar a iya sanin mu, da kuma tsananin binciken mu, tsakanin mu da Allah, mun fahimci cewa rigimar Gwamna da Sarki, Sarki ne mai gaskiya, shi yasa muke tare da Sarki kuma muke goyon bayan sa, tare da kokarin kare mutuncin sa da martabar sa.
Wasu da basu fahimci al’amarin ba, sun dauka cewa wai saboda wani abun duniya muke yin abun da muke yi; ba su san da cewa mu muna yi ne saboda soyayyar mu ga Sarki da kokarin kare gaskiya da masu gaskiya. Allah ya sani, muna son Mai Martaba Sarki tsakanin mu da Allah ba domin wani abun duniya ba. Kuma muna son sa ne don gaskiyar sa da kuma son sa ga gaskiyar, da kuma halaye da dabi’un sa nagari. Kuma mun yi Imani da cewa Allah ne kadai zai biya mu akan wannan abun da muke yi.
Alhamdulillahi, kuma jama’ah da dama sun fahimce mu, kuma sun gane abunda muke yi, kuma suna tare da mu, kuma suna goyon bayan mu, suna yi muna addu’o’i da fatan alkhairi a koda yaushe. Muna godiya a gare su matuka, muna rokon Allah ya bar mu tare, ya bar zumunci, amin.
Bayan wadannan, akwai wasu mutane ‘yan kalilan da ba su fahimce mu ba. Amma babu komai, su din ma har kullun, addu’a ta itace, Allah yasa su fahimci gaskiya, kuma ya ba su ikon bin ta, amin.
Wadannan mutane, suna kokarin yin batanci da cin mutunci da zagin mu, ba don komai ba, wai sai domin soyayya ta da goyon baya na ga Mai Martaba Sarki. Sun kira ni a waya, sun aiko da sako, sun yi rubuce-rubuce, akan wai suna mamaki, ta yaya ba zan goyi bayan wanda zai bani makudan kudade ba? Ni kuma har kullun ina shaida masu cewa, ni aiki na kare gaskiya da masu gaskiya. Kuma har kullun, shi mutunci yafi kudi a wuri na!
Wallahi, Allah shine shaida, rigimar Sarki da Gwamna, muna so ayi sulhu domin a zauna lafiya. Ba burin mu bane aci gaba da wannan fitina har abada. Amma kafin akai ga yin sulhun, mun fahimci cewa, akwai magoya bayan Gwamna da jama’ar sa da wasu gurbatattun ‘yan siyasa da magoya bayan su, wadanda suka mayar da wannan rigimar hanyar cin abincin su; wadanda har kullun, kokarin su shine, su bata Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II, su ci mutuncin sa, suyi masa karya da kage da sharri da kazafi. To mu kuma shi yasa muka ga cewa ba zamu yi shiru mu kyale su suna fada wa mutane karya ba, shine muka mayar da hankali wurin bayyana gaskiya da tona asirin wadannan mutane, tare da bayyana wa duniya gaskiyar al’amari akan Mai Martaba Sarki. Duk abunda wadannan mutane suke fada ko suke rubuta wa na makirci akan Sarki wallahi ba gaskiya ba ne! Kuma muna godiya ga Allah, mutane suna gane wa, suna fahimta, kuma suna tare da mu!
Haka nan fa kwanaki nayi rubutu akan irin nagartar tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da irin ayyukan alkhairin da yayi wa Najeriya na ci gaba, wanda ni wallahi yanzu haka bai san ni ba, watakila ma bai san nayi rubutun ba; da kuma rubutun da nayi akan Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III; ashe wannan rubutu bai yi wa wasu mutane dadi ba, shine suke ta surutu akai. To ni kuma ba su san cewa babu ruwana da surutun su ba. Ni kokari na shine, in bayyanar da gaskiya zuwa ga al’ummah, tare da nuna masu cewa abunda ake fada na batanci ga wasu mutane fa ba haka bane! Domin gaskiyar lamari shine, mutanen nan fa mutanen kwarai ne, mutanen kirki ne, salihai ne. Kawai mahassadan su ne suke kokarin yin batanci gare su domin cimma wata manufa ta rayuwar duniya. Wannan shine manufa ta, kuma Alhamdulillahi, mutane suna fahimta ta, kuma suna amsa kira na! Nagode wa Allah akan haka.
Shawara Ta Zuwa Ga Masoya Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II
Ya ku jama’ah! Ku sani, a yau, Allah ya kawo mu wani lokaci da makaryata su ka zamo masu gaskiya, masu gaskiya kuma suka zama makaryata, amma a wurin mutane marasa daraja. Don haka ya ku masoya Mai Martaba Sarki, dole sai kun zamo masu hakuri da wautar irin wadannan mutane idan Allah ya hada ku da su a ko’ina ne.
Ku sani, babban maganin irin wadannan mutane idan kun hadu da su, abu biyu ne:
Na farko, idan sun yi maku wauta da wawanci, to ku kada kuyi masu wauta, a’a, ku ku kyautata masu. Amma idan kun yi masu wauta kamar irin na su halin sai a kalle ku da sunan jahilai, domin da ma su an san cewa su jahilai ne.
Na biyu, idan sun fadi bakar magana ko wani batanci a kan Mai Martaba Sarki ko akan ku, to ku kar ku fada masu bakar magana, a’a, ku dai ku zane su da kyawon hali da kuma bayyana wa mutane gaskiyar al’amari ta hanyar ilimi. A daya gefen kuma kuyi ta fadawa Allah, ta hanyar addu’o’i, babu gajiya wa, Allah yayi maku maganin sharrin su da makircin su.
Idan kun zamo haka, to ko da sun je suna bata ku a cikin mutane, to su mutanen ne za su yanke hukunci, za su karyata su kafin ku ku karyata su!
A karshe kuma ina kira a gare mu dukkanin masoya Mai Martaba Sarki, da mu ci gaba da yiwa Mai Martaba Sarki Addu’a, Allah ya tsare shi, ya kare shi daga dukkanin sharri da makircin makiyan sa da magabtan sa, na zahiri da na badini.
Sannan dukkan wadanda suke nufin sa da sharri, Allah ya tattara masu sharrin su, ya mayar masu da sharrin su a kan su, amin.
Muna godiya a gare ku, ya ku masoyan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a duk inda kuke. Ina rokon Allah ya bar Sarki da Masoyan sa, amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za ku iya samun liman a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.