Za a gina asibiti, magudanan ruwa da manyan tituna a Buni Yadi jihar Yobe

0

Gwaman jihar Yobe Mai Mala Buni ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta gina sabbin asibitoci, magudanan ruwa da manyan tituna a garin Buni Yadi dake jihar.

Idan ba a manta ba garin Buni Yadi na daga cikin garuruwan da Boko Haram suka yagalgala a jihar sannan suka maida kusan kufayi.

Duk da cewa an kwato ikon garin daga Boko Haram, haryanzu garin na nan tsaye cak babu ci gaba.

Ya ce ce gwamnati za ta gina manyan tituna a garin sannan ra a gina magunan ruwa da sauran ababen more rayuwa.

“ Gina titunan da magudanar ruwa zasu ci akalla Naira miliyan 673,455,140.00.

Buni ya kuma ziyarci babban asibitin dake garin Buni Yadi inda yace gwamnati zata ci gaba da gyaran asibitin wanda asusun ‘Victim Support Fund (VSF)’ ta fara ginawa amma bata kammala ba.

Daga nan kuma Buni yace gwamnati za ta gina wasu tituna a garuruwan Babban gida da Damagum dake kananan hukumomin Tarmuwa da Fune.

“Ina kira ga mutane da su kiyaye zubar da shara a magudanar ruwa saboda a gujewa wa fadawa cikin matsalolin ambaliya.

Bayan haka shugaban karamar hukumar Gujba, Kyari Batrama ya yabawa gwamna Buni bisa kokari da maida hankali da yayi wajen ganin jihar ta ci gaba.

Mazauna garin Gujba sun yabawa gwamna Buni sannan sun yi masa fatan Alkhairi a ayyukan da ya sa a gaba.

Share.

game da Author