Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa, Babarunde Fowler, ya maida wa Shugaba Muhammadu Buhari ansa tambayar da ya yi masa a rubuce.
Buhari ya tambayi shugaban na FIRS dalilin da ya sa ba a samun kudaden shiga masu yawa, kamar cikin shekarun 2012 da 2014 a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan.
A cikin amsar da Fowler ya aika a Fadar Shugaban Kasa yau Litinin kamar yadda aka umarci ya yi, ya ce rashin samun kudaden shiga tun daga 2015 zuwa 2018 ya samo asali ne daga faduwar darajar farashin danyen mai a cikin 2015.
Sannan kuma ya ce faduwar farashin man ya haddasa karyar da darajar farashin kayayyaki.
Sai dai kuma Fowler ya ce idan aka yi la’akari da yawan kudin da Hukumar FIRS ke tarawa a bangaren harajin jiki-magayi da harajin game-gari, za a ga cewa FIRS ta fi tara makudan kudade a yanzu fiye da lokacin gwamnatin Jonarhan, a fannin kudaden shigar da ba na danyen man fetur ba.
Ya ce a zamanin gwamnatin Jonathan daidaikun mutanen da ke biyan haraji ba su fi milyan 10 ba kaf a fadin kasar nan.
A yanzu kuwa a ta bakin Fowler, ya ce masu biyan harajin VAT da sauran haraji a kasar nan sun kai milyan 20.
Idan ba a manta ba Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Shugaban Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida wasikar nuna damuwa dangane da tabarbarewa da karancin kudaden shiga a aljihun gwamnatin tarayya tun daga 2015 zuwa 2018.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES a yau Lahadi cewa wasikar wadda tuni ta karade shafukan soshiyal midiya, an rubuta wa Babatunde Fowler ita ce tun a ranar 8 Ga Agusta.
Ta na dauke da sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari. Ta na dauke da bayanai da tambayoyi kamar haka:
“An fahimci cewa ana samun daburtaccen kiyasi da kuma adadin kudaden harajin da ake tarawa tun daga shekarar 2015 har zuwa 2018. Wannan daburtattun adadin kudade sun kunshi na dukkan abin da ake yanka wa haraji na wadannan shekaru uku.”
An dai nada Fowler shugabancin Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida (FIRS) cikin 2015. Ya canji Samuel Odugbesan, wanda tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nada.
Kafin nada shi na kasa, Fowler ya rike Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Lagos, jihar da ta fi dukkan sauran jihohin kasar nan karfin arziki.
Nazari da bitar kudaden da Hukumar Tara Haraji ke tarawa a shekara kafin hawan Buhari da Fowler a 2015, ya nuna cewa a shekarar 2006 ce kadai FIRS ta kasa tara harajin da ta yi kiyasin samu a kasafin kudin ta.
Amma kuma wasikar nuna damuwar da aka aika wa Fowler daga Fadar Shugaban Kasa, ta yi bayanin shekarun 2012 da kuma 2014 kadai.
“Mun kuma fahimci cewa kudaden harajin da Hukumar FIRS ta tara a shekarar 2015 da 2017 ko kadan ba su ma kai na 2012 da 2014 ba.”
Haka wasikar wadda Abba Kyari ya sa wa hannu ta kara tuhumar Fowler.
“Don haka ana gayyatar ka da ka zo Fadar Shugaban Kasa ta yi bayanin dalilin da ya sa ba a samun kudaden shiga kamar yadda ya kamata a ce ana tarawa.”
A ranar Litinin 19 Ga Agusta ne aka umarci Fowler ya je ya yi bayani.