TARIN FUKA: An gano maganin cutar dake da inganci fiye da na da

0

Hukumar kula da ingancin magani da abinci ta kasar Amurka ta tabbatar da ingancin maganin kawar da cutar tarin fukan da baya jin magani mai suna ‘Pretomanid’.

Likitocin da suka gano wannan magani sun bayyana cewa saida ya dauke tsawon shekara daya suna gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin maganin a jikin mutum.

Sun kuma ce masu fama da tarin fukan da baya jin magani zasu yi watanni shida suna shan wannan magani kafin a warke.

Hukumar ta yi kira ga likitocin kan ci gaba da bincike domin rage tsawon lokacin shan magani da kuma tsadan farashin maganin.

Tarin fuka a Najeriya

Najeriya na daga cikin kasashe 14 a duniya da wannan cuta yayi wa katutu domin binciken ya nuna cewa Najeriya ne kasa ta shida a duniya da ke fama da cutar sannan kasar ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar a Afrika.

Bincike ya kuma nuna cewa mutane aƙalla 407,0000 ne ke kamuwa da wannan cuta a Najeriya duk shekara.

Domin dakile yaduwar cutar an shawarci Najeriya kan samar da kula na gari wa mutane 1,179,600 dake dauke da cutar.

Share.

game da Author