Kungiyar Harka Islamiyya, ta mabiya jagoran Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, IMN, ta yi kakkkausan bayanin abubuwan da suka faru ga jagoran na su, a kasar Indiya bayan saukar sa kasar da nufin zuwa a yi masa magani, shi da mai dakin sa Zeenat.
Ibrahim Musa, wanda shi ne Shugaban Masu Yada Labarai na IMN, ya fitar da bayani a rubuce, wanda kuma ya turo wa PREMIUM TIMES kai-tsaye.
A bayanin na sa, tunda farko ya ce ya na so ya yi karin haske dangane da abin da ya faru da su E-Zakzaky da matar sa tun daga farkon dirar su Indiya har zuwa lokacin dawowar su Najeriya, a yammacin yau Juma’a.
Sun sauka a filin jirgin sama na Abuja, inda Jim kadan bayan saukar su, jami’an tsaro suka yi wuf suka fice da su ta wata kofa daban.
IMN ta yi tir dangane da yadda jami’an tsaro suka hana ‘yan jarida yi wa jagoran na su tambayoyi bayan saukar sa filin jirgi.
Sun nemi a gaggauta sanar da su inda aka tafi da malamin na su.
IMN ta ce tun a nan gida Najeriya har a can kasar Indiya, gwamnatin Najeriya ta yi kokarin ganin cewa El-Zakzaky bai samu kulawar yi masa magani kamar yadda ya nema a yi masa a Indiya ba.
Har yau, IMN ta ce da hadin bakin gwamnatin Najeriya aka rika kuntata wa El-Zakzaky tare da cin zarafin sa da jami’an tsaro IMN din ta ce an yi a Indiya.
Kungiyar ta kuma yi bayani dalla-dalla yadda aka hana likitocin El-Zakzaky isa wajen sa a Indiya. Ta ce hats wani likitan sa ma da ya je daga Landan ba a bari ya gan shi ba.
Daga nan ta ce wadannan dalilan ne da kuma wasu suka sa malamin na su kin amincewa a duba lafiyar sa ko a yi masa magani da karfin tsiya a Indiya, bayan an ki amincewa likitocin sa su duba shi.
Daga nan sai suka yi tir da asibitin Medanta, tare da zargin cewa sun karyar dokar tsarin aikin asibiti, ta hanyar bari ma’aikatan asibitin na daukar hoton “selfie” tare da majiyyaci.
Ta kuma yi zargin cewa shiga cikin harkar maganin malamin da gwamnatin Tarayya ta yi, ya jefa zargi kan gwamnati cewa ta yi kokarin shirya kutunguilar kashe shi a kasar waje.
A karshe IMN ta ce za su ci gaba da fafitikar ganin cewa El-Zakzaky ya samu ‘yancin fita kasar waje neman magani a inda ya amince a kula da lafiyar sa.
ZA MU CI GABA DA ZANGA-ZANGA A FADIN DUNIYA, Inji AIM
Kungiyar Kamfen din neman a saki El-Zakzaky ta duniya, wato Free Zakzaky Global Campaign tare da hadin guiwar Ahlulbait Islamic Mission (AIM), sun fitar da sanarwar cewa su na umartar dukkan magoya bayan malamin a fadin duniya su ci gaba da zanga-zangar neman a saki jagoran mabiya Shi’a na Najeriya.
Sun fitar da wannan sanarwa a jiya Alhamis, inda suka ce ba za su gajiya ba har sai an bar El-Zakzaky ya fita neman lafiyar sa a inda ya amince a duba lafiyar sa.