ME YA YI ZAFI?: Lauya ya maka Buhari kotu, ya nemi hana shi rantsar da ministoci

0

Ranar Litinin ce Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja za ta yanke hukunci a kan wata kara da wani lauya ya shigar, inda ya nemi kotu ta hana Shugaba Muhammadu Buhari rantsar da sabbin Ministoci.

Lauya Musa Baba-Panya, ya shigar da karar ce a matsayin korafin rashin sunan dan asalin yankin Abuja, Babban Birnin Tarayya a cikin jerin sunayen sabbin Ministocin da Buhari ya nada.

Ya shigar da karar a ranar Alhamis da ta gabata, Baba-Panya ya shigar da karar, a matsayin sa na mai kara, har ila yau kuma lauyan da ke kare mai shigar da kara.

Ya nemi kotu ta tsaida Buhari, kada a bar shi ya rantsar da ministoci, saboda dokar da Baba-Panya ya ce ya karya, inda ya ki nada dan asalin yankin Abuja, Babban Birnin Tarayya a cikin jerin sunayen ministocin sa, kamar yadda dokar kasa ta tanadar.

Baba-Panya, wanda haifaffen Karu ne da ke karkashin Gundumar Yankin Abuja (FCT), ya shaida wa Babbar Kotun Tarayya a cikin kwafen karar da ya shigar cewa abin da Buhari ya yi ya saba da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta taba yankewa a ranar 15 Ga Maris, 2018.

Baya ga Shugaba Buhari, Baba-Panya ya hada har da Antoni Janar na Najeriya duk ya maka su kotu, inda ya roki kotu kada ta bari Buhari ya rantsar da su, kuma kada Antoni Janar ya tattabar da rantsuwar ta su.

A ranar 21 Ga Agusta ne Buhari zai rantsar da sabbin ministocin na sa 43.

A sammacin da Lauya Baba-Panya ya tura na shigar da kara, a ranar 7 Ga Agusta, wanda aka shigar kotu a ranar 8 Ga Agusta, ya rubuta cewa, “Ita kan ta amincewar da majalisa ta yi wa ministocin wadanda za a rantsar, haramtacciyar amincewa ce, an karya dokar kasa, ragabza ce, kuma bulkara ce aka tabka.”

“Buhari ya ci zarafin dokar kasa, ya raina kwansitushin da kotu, saboda irin yadda ya ki bin umarnin hukuncin Kotun Daukaka Kara na ranar 15 Ga Janairu, 2018.

“Wannan hukunci ya wajabta wa shugaban kasa ya rika nada dan asalin yankin Abuja, FCT a cikin jerin minsitocin Tarayyar Najeriya, kamar yadda doka ta tanadar.” Haka dai lauyan ya shigar a kotu.

Babayo-Panya ya je kotun ne tare da wani lauya, Sylvanus Tako, inda suka roki kotu ta amince da kukan da suka gabatar mata, ta hanyar sa wa Shugaba Buhari waigin hana shi rantsar da ministoci, har zuwa bayan ranar da kotu za ta yanke hukunci.

KADA A BAR BUHARI YA NADA ‘HARAMTATTUN MINISTOCI’

Ya rubuta wa kotun cewa idan aka bar shugaba Buhari ya rantsar da ministocin, “to ko ya nada minstocin sun zama haramtattun ministoci”

Baba-Panya ya ce tun daga komawa mukin farar hula cikin watan Mayu, 1999 ake tauye hakkin da dokar kasa ta bai wa Abuja FCT, kamar yadda ta bai wa kowace jiha cewa ita ma a zabo wani dan asalin yankin a nada shi minista, kamar yadda aka zabo ko aka dauko daga kowace jihar kasar nan.

Shi dai Buhari a cikin jerin ministocin nasa 43 babu dan asalin yankin Abuja ko daya, duk kuwa da cewa akwai ma wasu jihohin da aka dauko mutane biyu na aka bai wa mukaman minsta.

“Ni wannan kara da na shigar, ba tsakani na ne da Buhari ba, a’a, tun daga 1999 haka ake yi mana wannan zaluncin.” Inji shi.

Ya yi korafin cewa duk da dokar kasa ta ce akalla a dauko minista daya daga kowace jihar har da Abuja.

“Amma abin mamaki, sai ga shi Buhari ya dauko sunayen mutane har 43, ba ma 37 ba, kuma babu da asalin yankin Abuja da kewayen ta ko daya.

ABIN DA MAI KARA YA KE SON KOTU TA YI A KAN BUHARI

Kotu ta hana rantsar da sabbin ministoci.

Ko da an rantsar da su, kotu ta bayyana cewa haramtattun ministoci ne.

Kotu ta yanke hukunci, shin kaffarar rantsuwar kwansitushin ta kama Buhari ko ba ta kama shi ba?

Shin Buhari ya rantse da kwansitushin cewa zai bi doka ko bai rantse ba? Idan ya rantse, to ya karya doka da ya ki nada dan asalin yankin Abuja minista ko bai karya ba?

Shin idan wanda ake kara na farko, wato Shugaba Muhammadu Buhari ya karya wannan dokar, ya cancanci zama shugaban Najeriya ko kuma ci gaba da mulki, ko kuwa bai cancanci ci gaba da kasancewa shugaban kasa ba?

Idan bai cancanci ci gaba da shugabanci ba, mene ne makoma? Idan mai irin wannan karya doka ya ci gaba da mulki, kuma mene makoma?

Kotu ta yanke hukunci idan yankin Abuja, FCT ya cancanci a biya shi diyyar tauye masa hakki da aka yin a tsawon shekaru masu yawa, tun daga 1999.

Sai dai kuma Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya kori korafin cewa a haramta tantancewar da Majalisar Dattawa ta yi wa Ministocin.

Sannan kuma ya sa ranar 19 Ga Agusta, wato Litinin mai zuwa zai yanke hukuncin sauraren karar ko kuma a yi watsi da ita.

Share.

game da Author