Hukumar Kula da Yanayin Tumbatsar Ruwan Sama Da Nazarin Ambaliya (NIHSA), ta bayyana cewa alamomi da yawa na nuni da cewa za a yi fama da yawan ambaliya a cikin watan Satumba a Najeriya.
Babban Daraktan NIHSA ne, Clement Nze, ya tabbatar da wannan kakkausan jawabi a jiya Laraba, a lokacin da ya tara manema labarai ya ke musu bayani a Abuja.
Hukumar ta kuma zargi gwamnatin tarayya da alhakin kin daukar gargadin da ta sha yi a kan ambaliya a tun tuni a cikin wannan shekarar.
Daga nan ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su gaggauta ruguje duk wasu gini da aka yi a kan hanyoyin da ruwa ke wucewa.
NIHSA hukuma ce wadda aka dora wa alhakin bincike da sanar da yiwuwar barkewar ambaliya a Najeriya.
Wannan gargadi dai ya zo kwana biyu bayan da mahukuntan Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta sallami daliban ta zuwa gida cikin gaggawa, bayan da ambaliya ta halaka daliban jami’ar hudu a wurin kwanan dalibai.
PREMIUM TIMES ta ruwaito labarin cewa kananan hukumoni 74 daga cikin jihohi 30 a fadin kasar nan na fuskantar barazanar ambaliya mai karfin gaske, tsakanin watan Agusta zuwa Satumba.
Sanarwar ta kuma ce wasu kananan hukumomi 279 za su fuskanci ambaliya ba mai karfi ba.
Kwanan nan ambaliya ta tafi da wani darakta na Babbar Kotun Tarayya a Abuja, yayin da ruwa ya tafi da motar sa wadda ya ke ciki. Kuma har yau babu shi, babu labarin sa.
Ruwa ya tafi da daraktan ne cikin makon da ya gabata, a lokacin da ruwa ya cika karkashin wata gada da ke kuwa da shataletalen shiga Galadimawa a Abuja.
Wannan ce kuma ambaliya ta biyu da ta faru a wurin a cikin wata daya.
Idan ba a manta ba, tun cikin watan Oktoba, 2018 ne Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, wato NEMA ta bayyana cewa jihohi 12 za su fuskanci ambaliya.
Cikin wadanda ta lissafa kuwa har da yankunan da ke gefen Kogin Neja da na Benuwai.
Cikin wannan shekara dai Najeriya ta fuskanci sauyin yanayi sosai. Ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin-kwarya daga watan Yuli zuwa Agusta ya fara haddasa ambaliyarcda ke cin dukiyoyi da rayuka.