Kananan Hukumomi 74 na fuskantar barazanar ambaliya – Bincike

0

Hukumar Agajin Gaggawa ta Babban Birnin Tarayya, Abuja (FEMA), ta bayyana cewa bincike ya nuna akwai bazaranar barkewar ambaliya a kananan hukumomi 74 a fadin kasar nan.

Abba idris, wanda shi ne Babban Daraktan FEMA, ya bayyana cewa wani bincike ne ya tabbatar da haka.

Haka kuma ya bayyana cewa irin yadda Kogin Neja ke kara cika ya na batsewa da ruwa, zai iya zama babbar barazana ga Abuja, idan aka yi la’akari da kusancin birnin da kuma Lokoja.

Babban Daraktan FEMA, Abba Idris ne ya bayyana haka jiya Laraba a lokacin da ya ke jawabi wajen taron masu ruwa da tsaki a kan Hanyoyin Hana Afkuwar Ambaliya Da Kai Wa Ambaliya Daukin Gaggawa, wanda ya gudana a Abuja.

“Bayani daga Hukumar Nazarin Yanayin Ruwa ta bada sanarwar cewa a biya irin yadda ta ke nazarin cika da tumbatsar Kogin Neja tun daga ranar 8 Ga Yuli, ta lura cewa tuni har ya wuce irin cika da tumbatsar da ya taba yi a 2012 da 2018.

“Wannan bayani ya zo ne daidai lokacin da aka yi sanarwar cewa kananan hukumomi 74 a fadin kasar nan na fuskantar barazanar ambaliya.

“Ambaliyar da aka rika samu a Abuja kwanan nan, barazana ce da kuma damuwa sosai, musamman ga masu ruwada tsaki a kan karewa da magance afkuwar ambaliya a Abuja,’’

Idris ya ce wannan taro da suka yi wata dama ce da aka samu domin gagguta kawo dabarun yadda za a iya kaucewa da magancewa ko rage barnar ambaliya a yankin FCT, Abuja.

Daga nan kuma ya yi tsokaci da gargadi ga mazauna yankunan garuruwan Abuja su guji zubar da tulin shara da bola a hanyoyi da magudanan ruwa.

Yin hakan ya ce ya na toshe kwalbatoci da hanyar ruwa da sauran wasu aikace-aikacen da za su hana ruwa wucewa.

A na sa bayanin Babban Sakataren FCT, Chinyeaka Ohaa, ya bayyana cewa Hukumar Birnin da Kewaye da Abuja baki daya za ta ci gaba da rushe duk wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba, musamman wadanda ka yi a kan hanyoyin wucewar ruwan sama da ke kwarara a kasa.

Share.

game da Author