Yari ya yi barazanar maka wasu gidajen jaridu kotu

0

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya yi barazanar kai wasu kafofin yada labarai kotu, a bisa dalilin da ya kira sun buga labarai na bogi a kan sa.

Yari ya yi wannan barazana ce a cikin wata takarda da kakakin yada labaran sa, Ibrahim Dosara, a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Korafin da Yari ke yi dai ya biyo bayan wani samame da jami’an EFCC su ka kai a gidan sa na garin su, Talata Mafara, a jihar Zamfara.

Talata Mafara na kan titin zuwa Sokoto daga Gusau.

Jawabin da Dosara ya fitar a madadin tsohon gwamna Yari, ya ce wasu kafofin yada labarai uku sun buga labarin tare da baddala abin da ya faru da nufin bata wa Yari suna.

Ya buga misali da cewa batun an samu bargar motoci har guda 21a gidan Yari,ba gaskiya ba ne.

Ya ce jaridun da suka buga cewa Yari ya yi almubazzaranci da naira bilyan 2.35 daga kudaden mazauna sansanin gudun hijira, ba gaskiya ba ne.

Haka ma batun kudaden aikin zaizayar kasa da aka ce Yari ya karkatar har naira bilyan 3.51, su ma abin ba haka ya ke ba.

Dosara ya ce duk an danganta wadannan kudade da cewa EFCC ke zargin Yari da wawurar kudaden. Daga nan sai ya bada sa’o’i 24 da su gidajen jaridun su karyata kan su da kan su, sannan su ba Yari hakuri, ko kuma a maka su kotu.

Dosara ya ce ya na jira ya ga hukuncin da za a yi wa magulamcin da ya kantara wa EFCC karya, har suka kashi kafafu suka dira gidan tsohon gwamnan na jihar Zamfara.

Ya kara da cewa gidan Yari na Talata Mafara da aka ce an samu bargar motoci a ciki, ba shi ma da wadataccen filin da a za a ajiye motoci har 21.

Dosara ya ce me ya hana kafafen yada labaran su je su yi binciken naira bilyan 2.35 na Sansanin Masu Gudun Hijira da bilyan 3.51 na kudaden zaizayar kasa a hukumomin da ke da alhakin ba da kudaden kafin su buga labarin.

EFCC ta kai farmakin ne bayan Kwamitin Karbar Mulki daga hannun tsohuwar gwamnatin APC da sabon gwamna Bello Matawalle ya kafa, ta fitar da sakamakon binciken ta.

Kwamitin wanda tsohon mataimakin gwamna Yari, wato Ibrahim Wakkala ya jagoranta, ya yi ikirarin cewa Yari ya wawuri bilyoyin kudade, kuma ya bar wa jihar dimbin bashing da tulin kwangilolin da ba a kammala ba.

Share.

game da Author