APC ta zabi Hon. Doguwa Shugaban Masu Rinjaye

0

Jam’iyyar APC ta tsaida Alhassan Doguwa daga Jihar Kano matsayin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya.

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ne ya bayyana haka, a lokacin da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Gawuna ya shugabanci tawagar da ta kai masa ziyasa a Abuja.

Oshiomhole ya bayyana siyasa cewa abu ne da ake tinkaho da yawan jama’a, ya ce APC ta zabi Doguwa, domin jihar Kano ce ta fi kowace jiha samar wa APC kuri’u a zaben shugaban kasa.

“Don haka an ce alamun yawa kyauta shi ne a bayar da tukuici. Jihar Kano ta bai wa APC dimbin kuri’u a zaben shugaban kasa. Dalilin haka dole mu yi mata sakayya.

Ba don wadannan yawan tulin kuri’u daga jihar Kano ba, da ba mu yi nasara ba. Idan ka dubi ratar da ke tsakanin Shugaban Kasa da ta wanda ya zo na biyu, wato Atiku, idan ka cire kuri’un jihar Kano ratar za ta ragu sosai. Inji Oshiomhole.

Sai ya ce idan da adadin wadannan tulin kuri’u sun fada a daya bangaren to da labari ya sha bamban kenan.

Daga nan sai ya ce ba za a taba mantawa da kokarin da Kano ta yi ba wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC ta sake mulkin kasar nan a zaben 2019.

Da ya koma kan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Oshiomhole ya ce APC na tutiya da irin mulkin da gwamnan ke gudanarwa a Jihar Kano.

Tun da farko sai da Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna ya jinjina wa APC kuma ya yi godiya a kan damka wa Doguwa shugabancin masu rinjaye da aka yi a Majalisar Dattawa.

A Majalisar da ta gabata, Doguwa shi ne Bulaliyar Majalisa, wato Mai Tsawatarwa.

Share.

game da Author