Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta bada sanarwar kama wasu matasa uku da ke da hannu wajen yin garkuwa da wani yaro, sannan suka kashi.
Yaron dan shekaru biyar da haihuwa mai suna Ahmad Ado, wadansu matasa ne, Ibrahim Ahmad mai shekara 20, Abdulmajid Mohammed dan shekara 18, sai kuma Musa Sanusi dan shekara 20 suka kama shi.
Kwamishinan ‘Yan Sanda Iliyasu na Jihar Kano, ya shaida wa manema labarai haka a lokacin da ya ke gabatar da matasan a gaban ‘yan jarida.
Ya ce a ranar 10 Ga Yuli, wajen karfe 1:30 na rana jamai’an sa suka samu rahoto daga unguwar Karkasara, a Kano cewa wasu da ba san ko su wa ba ne, sun yi garkuwa da wani yaro a Makarantar Islamiyya ta Ma’ahad da ke Karkasara.
Ya ce bayan sun kama yaron, sai suka tuntubi iyayen sa, inda suka nemi a biya diyyar naira milyan 50 kafin su sake shi.
Iliyasu ya ce jami’an tsaro na ‘Operation Puff Adder’ daga rundunar dakile garkuwa da mutane suka shiga aikin yadda za su kama masu laifin.
Sun yi amfani da na’urori da waya ta hanyar kama wadanda suka yi garkuwar.
Wadanda aka kama din sun shaida wa ‘yan sanda cewa an bai wa yaron kwaya bayan sun yi garkuwa da shi, wanda hakan ne ya haifar da mutuwar sa a cikin wani kango a unguwar Sheka Sabuwar Gandu, a Kano.
“Wadanda ake zargin sun gina rami a bayan kango suka binne yaron.
“Jami’an mu sun je har inda suka binne yaron, suka tone shi, suka dauko shi.”
A bayanin da ya yi wa ‘yan jarida, daya daga cikin masu garkuwar ya ce shi ne ya sato yaron daga makaranta, kuma ya damka shi ga masu garkuwa.
“Daga nan sai suka ce min kada na je cikin kangon da suka boye shi, don kada ya shaida ni, tunda ya san ni.
“ Sun ba shi kwaya ya sha ne, kuma suka sa saletef suka manne masa bakin sa, shi ne ya mutu. Daga nan suka gina rami suka binne shi.” Inji shi.
Iliyasu ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.
Daga nan ya gargadi jama’a da su rika yin kaffa-kaffa da abokai da mukasantan su, domin wasu mugaye ne ba a sani ba.
Wani da wakilinmu ya zanta da shi, ya tabbatar da cewa makarantar Ma’ahad ba ta da nisa da gidan sa. Kuma makaranta ce mai rasa da dama a cikin unguwar.
Wakilin mu ya tabbatar da cewa Ma’ahad ba ta da nisa da gidan Sheikh Ahmad Sulaiman, Alaramman Kungiyar Izala da aka taba yin garkuwa da shi a jihar Katsina.