Kwamandan rundunar sojin dake fafatawa da Boko Haram, Benson Akinroluyo bude kotun hukunta sojojin da suka aikata laifuka.
Akinroluyo ya bude kotun ne ranar Alhamis ganin cewa akwai sojojin da suka aikata laifuka dabam da abam har 21 da ya kamata a hukunta su.
Saidai kuma Akinroluyo bai bayyana laifukan da wadannan sojoji suka aikata ba amma bayanai sun nuna cewa sojojin da aka hukunta a baya a irin wannan kotu sun aikata laifukan da suka hada da fyade, siyar da makamai wa ‘yan fashi da makami, barin aiki ba tare da izini ba, sata, cin zarafin yara da sauran su.
Yace ya bude wannan kotu ne bisa ga iko da yake dashi na karfin ofishinsa sannan ya tabbatar da cewa ba za a nuna son kai ba.
Akinroluyo ya yi kira ga shugabanni da alkalan kotun da su yi aiki ba tare da nuna fifiko ba.
“ Ina da masaniya game da laifukan da sojojin suka aikata sannan lissafa laifukan sojojin aikin kotun ne ba nawa ba.”
Discussion about this post