Kotun Daukaka Kara ta shiyyar Abuja, ta kori karar zargin rashin cikakkun takardun sakandaren Buhari, wadda ake kalubalantar cancantar tsayawar sa takarar zaben 2019.
A yau Juma’a ne alkalan kotun su uku suka yanke hukuncin cewa an shigar da karar ce bayan an daina saurare ko karbar kararrakin lamarin da ya shafi abubuwan da ke da la’aka ko nasabar kafin zabe.
Dama dai ranar Laraba da ta gabata ne alkalan a karkashin shugabancin Mai Shari’a Atinuke Akomolafe-Wilson suka aza ranar yau Juma’a da za su yanke wannan hukunci.
Mutane uku ne, Kalu Kalu, Labaran Isma’il da kuma Hassy Kyari suka maka Shugaba Buhari kara cewa bai cancanta ya tsaya takarar shugaban kasa ba.
Da farko sun shigar da karar a Babbar Kotun Tarayya, wadda ta kori karar. Daga nan kuma sai suka garzaya Kotun Daukaka Kara, inda nan ma a yau a ka sake korar karar.
Da ya ke karanta hukuncin da kotun ta yanke a madadin sauran alkalai biyu, Mai Shari’a Mohammed Idris ya ce ta su amince da dalilan da Babbar Kotun Tarayya ta bayar na korar karar, don haka ita ma ta yi fancakali da karar.
Alkalan sun ce sun yi amfani da Sashe na 285 (9) na Dokar 1999 cewa an gabatar da karar ba a cikin hurumin kwanaki sha hudu da suka wajaba a kai karar duk wani korafin da ya taso daga tankiyar al’amurran kafin ranar zabe ba.
A kan haka ne suka ce wannan kara ba ta da hurumi ko wata hujjar da za a iya karba, saboda matsalar lokacin da aka shigar da karar ya zarce ka’idar wa’adin da doka ta tanadar.
Wannan matsala ta takardun shaidar sakandaren Buhari na daga cikin hujjojin da PDP da Atiku Abubakar suka gabatar a karar da suka shigar inda su ma suke kalubalantar cancantar tsayawar Buhari zaben 2019, da kuma zargin cewa APC ba ta ci zabe ba, amagudi aka yi aka bayyana cewa ita ce da Buhari suka yi nasara a zaben shugaban kasa na 2019.