Jami’in asusun kula da al’amuran kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Bioye Ogunjobi ya bayyana cewa wanke hannu da ruwa ba tare da Sabulu ba baya kau da dattin a hannu.
Ya ce rashin amfani da sabulu da ruwa wajen wanke hannun musamman bayan an fito daga bayan gida shine ya fi dacewa ba da ruwa ba kawai.
Ya kuma yace kafin a ci abinci da bayan anci a wanke hannu da ruwa mai tsafta da sabulu domin samun kariya daga kamuwa da cututtuka.
A kwanakin baya ne ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa wanke hannu da ruwa da sabulu na kare mutum daga kamuwa daga mugan cututtuka.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne a taron mai taken ‘ Tsaftattacen hannaye, mabudin samun ingantaccen kiwon lafiya” da aka yi a Abuja don wayar da kan mutane game da mahimmancin wanke hannu.
A wajen Taron Kamfanin ‘Detol’ ya yi kira ga iyaye da malaman makarantu da su rika koya wa yara ‘yan makaranta dabi’ar wanke hannu a kowani lokaci.