Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Gambo Gumel Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar NACA ta kasa.
Hakan ya biyo bayan ajiye aiki da shugaban hukumar Sani Aliyu yayi ne yau.
Babban Sakatare a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Olusegun Adekunle ya bayyana cewa nadin ya yi daidai da dokar kasa sannan yace nadin Gambo Gumel ya fara aiki ne tun a ranar 26 ga watan.
Kafin nadin Sani Aliyu, yana aiki ne a Kasar Birtaniya.
