Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Kamar yadda duk kuka sani, kuma kuka karanta, labari mara dadi, mai sosa rai yana nan yana ta yawo a kafafen yada labarai na yanar gizo da na zamani, cewa wai ranar Asabar din nan da ta gabata mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, wato Hajiya Amina Muhammed ta wallafa wani sako a shafinta na twitter cewa tana goyon bayan ‘yan luwadi da ‘yan madigo a duniya.
Wannan magana da ake zargin Hajiya Amina Muhammed tayi ta jawo cece-kuce da kace-nace sosai a shafukan sada zumunta, a inda mutane da yawa suke Allah wadai da wannan furuci nata.
Saboda matukar yaduwar wannan zance yasa ba zai taba yiyuwa ayi shiru da maganar ba, a manta da ita, kamar yadda wasu ‘yan uwa suke kokarin nuna muna. Kawai dai hayaniyyar banza marar amfani shine bai dace ba sam. Amma tattauna al’amarin domin samar da mafita ba laifi ne ba. Allah yasa mu dace, amin.
Tsakani da Allah, a lokacin da ake ta surutai game da wannan al’amari, ni naja baki na nayi shiru ne ban ce komai ba, nayi shiru ne ba don komai ba sai don tsammanin watakila ita wadda ake zargin zata ce wani abu ko tayi magana akan zargin da ake yi mata din, shin ta fada ko bata fada ba. Ba wani abu yasa na dauki wannan mataki ba sai don sanin yadda muke yiwa juna sharri, karya da kage a kafofin sada zumunta a yau.

Har nayi wani dan karamin bayani na tura a kafafe da dama na sada zumunta domin dai kokarin nemar wa wannan baiwar Allah, ‘yar uwar mu uzuri, amma dai a iya mutanen da na tuntuba, kuma na zanta da su, sun nuna mani cewa lallai wannan baiwar Allah, wato ‘yar uwa Hajiya Amina Muhammed ta fadi wannan magana, domin a inda ta rubuta wannan magana, wato a twitter, shafin nata ne bana wani ba ne.
A cikin bayanin da na rubuta nike cewa:
“Ya kamata a rinka daukar matakin kwakkwaran bincike kuma ana nemawa mutum uzuri da nasiha kafin a fara kai masa hari a social media. Sannan ina rokon don Allah a samu wasu bayin Allah da suke da hanyar yin magana da Hajiya Amina Muhammed, su yi kokarin jin ta bakin ta, shin da gaske ne ta fadi wannan magana mai hadari ko ba ta fada ba!”
Sanadiyyar haka ne na yanke shawarar yin wannan rubutu domin jawo hankalin ‘yar uwar mu, wato Hajiya Amina Muhammed, da cewa don Allah ina kira a gare ta da ta ji tsoron Allah a cikin aikin ta da dukkanin al’amurranta. Ta sani cewa fa ita Musulma ce, kuma addinin ta na Musulunci ya hana kuma ya haramta auren jinsi. Sannan bayan hanin da addinin ta yayi, ta sani, al’adarta da kuma yankin da ta fito duk sun haramta kuma sun tsani wannan al’amari, kuma ba ta wannan hanyar ba ce suke samar da zuri’ar da ita tana cikin su. Kuma ta sani cewa, al’adunta da addinin ta sun saba da wadancan turawa da take aiki tare da su, don haka sai tana yi tana taka-tsan-tsan a wurin aikin ta, domin ba komai ne zasu yi ita ma tace sai tayi hakan ba.
Sannan kuma ya zama wajibi ‘yar uwar mu Hajiya Amina Muhammed ta sani, lallai ‘yan luwadi da ‘yan madigon nan mutane ne da suka kauce wa dabi’ar da Allah ya halicci ‘yan Adam a kan ta, wato hanyar mace da namiji su auri juna su ji dadin junansu, kuma su samar da zuri’ah dayyaba, wadda Allah da Manzon sa (SAW) za su yi alfahari da ita. Kai ko dabbobi ma masu hankali basa yin abinda ‘yan luwadi da ‘yan madigo suke yi, na mace-ta-nemi-mace, namiji-ya-nemi-namiji.
Don haka duk wanda ya kauce wa dabi’ar da Allah ya halicce shi a kan ta, ya fada wata hanya da ba ta dace ba, ta madigo da luwadi, to lallai dabbobi ma sun fishi tunani da hankali. Sannan wadannan mutane suna cikin masu haifar da musibu a cikin al’ummah.
Ina kira ga ‘yar uwa Hajiya Amina Muhammed ta sani, yaduwar luwadi da madigo a cikin al’ummah ya jawo karin yaduwar cututtuka masu wahalar warkarwa, kamar cutar KANJAMAU, da yake karya garkuwar jikin Dan Adam, da sauran cututtuka masu hadarin gaske ga lafiyar ‘yan Adam.
Sannan wadannan miyagun dabi’u suna jawo matsalar zamantakewar iyali, suna jawo kasala da ragwanci a cikin al’ummah, har a wayi gari al’ummah ta zama sokuwar al’ummah da sauran al’ummomi suka yiwa fintinkau. Sannan suna jawowa al’ummah karin jahilci da yin watsi da harkar ilimi da ilimantarwa.
Kai ko da ace luwadi da madigo basu haifar da wata illa a cikin al’ummah, ya zama wajibi Musulmi ya nisance su, tun da mahaliccinsa ya hana shi. Kuma muna sane da cewa, duk abunda Allah ya hana wallahi barin sa shine alkhairi a gare mu, aikata shi kuwa sharri ne da zai iya rusa zaman lafiyar al’ummah da ci gaban ta.
Imam Ibnil Qayyim Al-jawziyyah yana cewa:
“Zina, luwadi da madigo suna tattare da zubewar mutunci da kuma wulakanci da suke sa mutum ya kaucewa manufar Allah a kan sa. Kuma sun kasance manya-manyan zunubai abin kyama a wurin Allah. Sannan suna tattare da sharri da cutar da ta kai ace mutum ya rasa rayuwar sa ta hanyar kisa da ace an aikata wannan a kan sa. Saboda duk mutumin da ya dauki wannan hanya ta lalacewa, to ya zama sharri da guba a cikin al’ummah. Za’a wayi gari baya jin kunyar Allah baya jin kunyar mutane. Kuma shiriya za ta yi wahala a wurin irin wannan mutum, sai fa idan Allah ne ya nufe shi da shiriya. Maniyin da aka zuba wa mutum a jikinsa ta hanyar zina, madigo ko luwadi, guba ne a cikin jikinsa kuma dafi ne mai cutarwa. Shi yasa malamai suka yi sabani cewa, shin mai aikata irin wannan aiki zai shiga Aljannah kuwa? Akwai maganganun malamai guda biyu kamar yadda Ibn Taimiyyah ya fada.” [Duba Jawabul Kaafi, shafi na 115]
Ya ke ‘yar uwar mu mai daraja, ki sani fa madigo shine mace ta nemi mace ‘yar uwarta, domin taji dadi da ita, ta gamsar da ita ta yadda namiji zai gamsar da ita.
Madigo wanda a turance ake kira da lesbianism yana nufin saduwa ta hanyar gogayya tsakanin mace-da-mace ta amfani da halittarsu, domin kauda sha’awar junan su. Idan wannan ya kasance a tsakanin namiji da namiji to ya koma luwadi kenan. Wal iyazu billah!
Sannan neman jinsi ya faro ne tun daga zamanin Annabi Lut (AS). Wanda tarihi ya nuna cewa shaidan ne yazo a cikin siffar ‘yan Adam, ya nuna wa mutanen Annabi Lut (AS) yadda zasu rinka neman junan su.
A yau, an wayi gari duniyar kimiya da fasaha musamman duniyar yanar gizo (internet), na daya daga cikin hanyoyin da ke koyar da wadannan munanan dabi’u, musamman a social media, inda zaka tarar a can da suna yi a boye, yanzu kuwa sun fito fili har groups su ke da shi daban-daban a Facebook, WhatsApp da sauran su. Wani abin takaici shine, sai ka tarar mafi yawansu duka hausawa ne, Musulmai, ‘yan arewa. Wannan sharrin yahudawa ne, kuma sannu a hankali suna samun nasara a kan mu!
Madigo da luwadi wata mummunar dabi’a ce da ko dabbobi masu hankali basa neman junansu, amma sai gashi ya bayyana ga ‘yan Adam. Allah ya la’anci mai yin sa. Kuma wanda duk Allah ya la’ana to wallahi babu shi babu albarka a rayuwar shi. Kuma babu shi babu samun alkhairin duniya da na lahira.
Mala’iku suna da hankali amma basu da sha’awa. Mutane suna da sha’awa kuma suna da hankali. Su kuwa mafi yawan dabbobi suna da sha’awa amma basu da hankali. A nan, a duk lokacin da hankalin dan Adam ya rinjayi sha’awarsa to sai ya koma daga cikin mala’iku, domin sune ke da hankali amma basu da sha’awa. Idan kuwa sha’awar Dan Adam ta rinjayi hankalin sa to sai ya koma daga cikin dabbobi, domin sune ke da sha’awa amma basu da hankali.
Madigo da luwadi musiba ce ta shigo cikin al’ummah wadda zata iya haddasa kowane irin fushin Ubangiji. A yau bala’o’in da muke ji suna faruwa a wasu kasashen waje, kamar girgizar kasa, iska da tsawa gami da kashe-kashe da yake-yake da zubar da jini babu kakkautawa, gasu nan biye da mu, ba domin komai ba, sai don wadannan miyagun ayyukka da ke gudana a cikin al’ummar mu.
Ta fannin zamantakewa da kiwon lafiya kuwa, hakika akwai illoli masu yawa da madigo da luwadi ke haifarwa a jiki kamar haka:
1. Su na kawar da sha’awar aure baki daya. Domin a addinance da kuma al’adance akan daura aure ne tsakanin mace da namiji. To macen da take madigo zata kasance bata sha’awar namiji baki daya. Ko tayi auren, tayi ne kawai, amma ba zata yi sha’awar mijin ba.
2. Ba zata sami biyan bukata a kwanciyar aure ba. Shi kuma jima’i a tsakanin ma’aurata, yana kara gina so da kauna a tsakanin juna. Koda an sadu da ita, to ba zata ji sha’awarta ta gushe ba har sai ta hadu da ‘yar uwarta mace sun goga da juna. Shi yasa kake ganin matan aure na aikata wannan mummunar dabi’ar.
3. Madigo na haifar da yaduwar ciwon sanyi. A duk lokacin da wadda take dauke da ciwon sanyi tayi tarayya da wadda bata da shi, to anan zai yadu. Domin wannan discharge din yana dauke da kwayoyin cuta da zai yadu ya shafe ta.
4. Madigo yana haifar da cututtukan da ke sa kaikayi ga farjin mata. Idan mai kaikayin mara ko kuraje a cikin farji ko zubar farin ruwa, sanadiyyar wani infection, kamar na vulvo vaginal candidiasis, yeast infection, da sauran su, idan suka yi gogayya da juna, to zata dauki wannan ciwon.
5. Madigo yana haifar da yaduwar cutar Kanjamau/Sida (wato AIDS). Kuma ban ga yadda za’a kare wannan kwayar cutar ba, domin takan biyo ruwan dake fitowa a gaban mace ta shafi ‘yar uwarta, kuma ba za’a iya yin amfani da condom ba, kuma ma bincike ya nuna cewa Condom ba ta iya kare komai. Kawai magani shine, aji tsoron Allah a daina (Abstinence).
6. Madigo yana haifar da ciwon mara – Dama, su mata sun fi kowa yawan ciwon mara, wasu ma da shi aka haife su, wasu kuma a lokacin al’ada yake zo masu, wasu kuma daga baya suka dauko shi a wani wuri (infections). Gogayyar da suke yi gaba-da-gaba da juna na haifar da kamuwa da ciwon mara, musamman na infections. Ayi ta faman neman magani a rasa sanin dalili.
7. Madigo yana haifar da ciwon ruhi (spiritual problems) – A nan, shi ciwon ruhi ba fa ciwo bane da zaki gani a zahiri, amma a hakika zaki ji alamunsa a gangar jikin ki. Na farko dai zai busar da zuciyar ki, sai ya kasance baki shakku ko tinanin zaki iya mutuwa a kowane lokaci. Sha’awarki zata gushe ta koma ga ‘yan mata kawai. Da zaran kin ga mace mai girman kirji ko mai manyan duwawu duk sai sha’awarta ta kama ki. Sannan komai nisan ki da ita zaki iya neman ta. Har ki tsufa zaki kasance kina ganin sha’awar mata ‘yan uwanki.
8. Sirrance zai janyo maki gushewar farin jini a fuskar maza, sai kiga duk masoyanki mata ne, gaki kyakkyawa amma ba mai so, basirar ki tabi ta dushe, tunanin ki ya sauya. Wata rana sai ki kasa daina wa. Kuma zuwa gaba sai ya busar da ke, ki rinka ramewa, duk ni’imar jikin ki ta mace, ta gushe, kibi ki bushe, kiyi matukar muni. Kuma a lokacin sai kiyi dana-sani, a lokacin da dana-sanin ba zai amfane ki ba! Allah ya shirye mu baki daya, amin.
Don haka ina kira ga Malamanmu da Masarautunmu da Gwamnatocinmu da likitocinmu da masana hakayyar ‘yan Adam (Psychologists) da Hukumomin kula da harkar fina finai da kuma Matasanmu masu kishi da dukkanin masu ruwa da tsaki wurin ci gaban wannan al’ummah da zaman lafiyar ta, da mu tashi tsaye baki daya, mu hada karfi-da-karfe mu yaki wannan mummunar al’ada ta luwadi da madigo a cikin al’ummah, kafin mu jawo wa kan mu fushin Allah!
In ban da toshewar basirah da kuma kokarin yin fito-na-fito da Allah ba, wai ace namiji ya kwanta da namiji dan uwansa ko kuma mace ta kwanta da mace yar’uwarta!!
Ya zama dole a kan mu, mu tashi muna tallata addinin mu da al’adunmu, bawai turawa ne zasu ringa yi muna tallan al’adunsu ba, balle suyi muna tallar al’ada irin ta luwadi da madigo.
Allah ya halakar da mutanen Annabi Lut, ya kuma nuna wannan mummunar alfasha ce wadda ba wanda ya fara a duniya in ba su ba. da yake bayanin yadda ya halakar da su, ya nuna muna ruwan duwatsu da Allah yayi masu ba babba ba yaro, duk aka halakar da su.
Manzon Allah (SAW) ma a Hadisin Ibn Abbas (RA) a lokacin da yake jero wadanda Allah ya tsine masu, har yazo kan ‘yan Luwadi’, ya tsine ma duk masu aikin (luwadi), irin aikin da mutanen Annabi Lut suka yi.
Ina fatan duk masu irin wannan hali Allah ya shiryar muna da su, mu kuma Allah ya kare mu daga irin wannan mafi munin aikin dabbanci, Amin.
Wassalamu Alaikum
Dan uwan ku:
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nijeriya. Za’a iya samun Imam ta adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.
Discussion about this post