Gwaman jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa gwamnati a shirye take ta karbi ‘yan gudun hijira 4,000 ‘yan asalin jihar da ke samun mafaka daga Kamaru.
Fintiri ya fadi haka ne da yake ganawa da tawagar dawo da ‘yan gudun hijira daga kasar Kamaru da suka kawo masa ziyara.
Gwamnan ya ce zai kafa nashi kwamitin kula da walwalansu domin hada hannu da kwamitin kula da walwalan ‘yan gudun hijiran dake jihar domin amsar su.
Ya kuma jinjina wa kokarin da kasar Kamaru ta yi wajen kula da ‘yan gudun hijiran dake samun mafaka a kasar.
Jagoran tawagar kuma kwamishinan a kwamitin gwamnatin tarayya na hukumar kula da ‘yan gudun hijira na kasa da kasa Sadiya Farouk ta bayyana a Yola cewa sun ziyarci gwamnan ne domin sanar masa da shirinsu na dawo da ‘yan gudun hijira ‘yan asalin jihar daga kasar Kamaru.
Sai dai kuma Sadiya bata fadi ranan da aka tsayar don dawo da ‘yan gudun hijiran amma ta shaida cewa nan ba da dadewa ba za a fara dawo da ‘yan gudun hijiran zuwa jihar daga kasar Kamaru.
Idan ba a manta ba Hukumar kula da ‘yan gudun hijira na kasa da kasa (NCFRMI) ta bayyana cewa za ta dawo da ‘yan gudun hijira 91,000 ‘yan Najeriya da ke samun mafaka a kasar Kamaru.
Jami’in hukumar Lawal Hamidu ya shaida wa manema labarai cewa kasar Kamaru za ta dawo da wadannan ‘yan gudun hijira ne bisa ga yarjejeniyar da ta yi da Najeriya.
Hamidu ya ce kasar Kamaru ta tsara shiri don ganin cewa wadannan ‘yan gudun hijira sun dawo kasar su cikin koshin lafiya.
“Cikin ‘yan gudun hijiran 91,000 din da za a dawo da su 4,000 yan asalin jihar Adamawa ne,sannan 87,000 daga jihar Barno.”