Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi karin hasken cewa akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen ministaocin sa a cikin wannan makon.
Tun ranar 29 Ga Mayu aka sake rantsar da Buhari a karo na biyu, amma har yau bai nada sabbin ministoci ba.
Wannan tsomomuwa ta jefa mutane da dama cikin damuwa, wadanda ke ganin cewa babu wani dalilin da zai sa Buhari ya shafe wannan lokaci bai nada sabbin ministoci ba.
Sannan kuma da dama su na tuna yadda a zangon sa na farko sai da ya shafe watanni shida kafin ya lalubo sunayen wadanda ya nada ministoci.
Sanata Bassey Akpan na jam’iyyar PDP, kuma daga jihar Akwa Ibom, ya yi kira Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da ya gaggauta nuna wa Buhari muhimmancin nada ministoci da wuri. Ya ce yin hakan ya na daga cikin ayyukan da su ka wajaba shugaba ya rika gudanarwa ko aiwatarwa a cikin hanzari.
“Saboda kalandar hutun majalisa ta nuna cewa nan da makonni biyu za mu tafi hutu. Kuma kowa ya san cewa majalisa ta amince cewa za a maida fasalin tsarin aiwatar da kasafin kudi daga watan Janairu zuwa Disamba.”
Akpan ya ce idan Buhari na irin wannan tafiyar hawainiyar, to ba za a iya cimma wannan burin daidaita watannin kasafin kudi ba.
Ya na cikin cewa ya kamata Buhari ya gaggauta aiko musu da sunayen ministoci, sai majalisar ta kaure da hayaniya.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana musu cewa ana nazarin sunayen ministocin, kuma ya na sa ran za a aiko su majalisa a cikin wannan makon.
Discussion about this post