Dalilin goyon bayan masu ‘Madigo’ da ‘Luwadi’ yasa ba zan ziyarci Saudiyya ba – Inji Minaj

0

Shahararriyar mawakiyar nan ‘yar kasar Amurka, Nicki Minaj, ta bayyana cewa ba za ta ziyarci kasar Saudiyya kamar yadda a ka sanar a makon jiya.

Minaj zata yi wasa ne a filin wasa na Sarki Abdullah dake Jedda kafin ta canja shawarar ba za ta halarci bikin casun ba.

Babban dalilin da ya sa Minaj ta canja shawarar duk da gayyatar ta da kasar Saudiyya ta yi mata shine don goyon bayan kungiyoyin kare ‘yan cin mata masu madigo da masu Luwadi da take yi, kuma gashi kasar Saudiyya ta haramta hakan.

Mutane da dama na sun yi ta tofin Alla tsina ga wannan shiri na gwamnatin kasar Saudiyya cewa shirya irin wannan buki bai kamata a ce kasa kamar Saudiyya za ayi shi ba, inda ake zuwa aikin Hajji sannan kuma a wannan kasa ne Kabarin Annabin Tsira Mohammadu SAW yake ba wai kuma za a yi irin wannan tambadewa a ciki.

Masu shirya wannan buki sun ce ba za a siyar ko a sha giya ko muggan kwayoyi a wannan wurin rawa ba.

Idan baa manta ba tun a wancan lokacin wasu daga cikin kawaye, da abokan Minaj suka rika ja mata kunne cewa kada ta ta tafi kasar casu.

Share.

game da Author