Masu garkuwa sun kashe ‘Yar shugaban kungiyar Yarabawa na Afenifere

0

Kungiyar Yarabawa na Afenifere ta sanar cewa masu garkuwa sun kashe ‘Yar shugaban kungiyar Reuben Fasoranti a hari da suka kai wa motar su.

Kakakin kungiyar Yinka Odumakin ya bayyana cewa Funke Olakunrin, mai shekaru 58 ta rasu ne bayan wasu masu garkuwa dauke da bindigogi sun bude wa motan da take ciki wuta.

Wani da abun ya faru a idonsa ya ce Fulani ne suka tare motar a hanyarsu na zuwa garin Ore daga Akure.

Sun harbi Olakunri da hakan yayi sanadiyyar rasuwarta.

Masu garkuwan sun tattare wasu motocin.

Share.

game da Author