KOGI: APC ta amince ta yi zaben fidda gwani a asirce

0

Kakakin jam’iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu ya bayyana cewa uwar jam’iyyar a Abuja ta amice da ayi zaben fidda gwani na jihar Kogi a asirce.

Wasu ‘Yan takarar gwamnan jihar a inuwar jam’iyyar da wasu jiga-jigan jam’iyyar sun nemi jam’iyyar ta gudanar da zaben fidda gwani na gwamnan jihar ta hanyar kato a bayan kato maimakon a asirce.

Sai dai uwar jam’iyyar ta ce za a gudanar da zaben fidda gwanin ne ta hanyar kowa da Kuri’ar sa wato a asirce.

Gwamnan jihar Yahaya Bello na jam’iyyar APC na neman ta zarce, amma kuma babban abokin hamayyarsa kuma dan tsohon gwamnan jihar Marigayi Abubakar Audu, Mona Mustapha Audu ya dage sai ya kada Yahaya Bello din a takarar.

Wasu da dama na ganin muddun ba a iya yin abinda ya kamata ba akwai yiwuwar cewa jam’iyyar APC zata sha kayi a zaben gwamnan.

Saidai kuma ita kanta jam’iyyar PDP din acike take da hayaniya domin ‘Yan takara da yawa ne suka wasa wukaken su domin neman kujeran gwamnan jihar ciki kuwa har da fitaccen sanatan nan, Dino Melaye.

Share.

game da Author