TAMBAYA: Shin awane lokaci akeyin Niyyar a alwala? Tare da Imam Bello Mai-Iyali
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Hakika musulmai da yawa suna barin sallar su tun a gurin alwala. Niyya
wajiba ce a alwala kuma ana yenta ne ayayin wanke fuska ba a farkon
alwalaba. Mai alwala zai kudurce Niyyar alwalar sa a cikin zuciyar sa yayin wanke fuskar sa. Musulmin da baiyi Niyya a muhallinta ba yana cikin hadari.
Amma a farkon alwala mutum zaiyi nufin ibada ne a lokacin wanke hannunsa.
Lalle ne mukoma makaranta domin fahimtar yanayin da yakamata musulmi yayi Ibadarsa.
Allah ya tsare mana imanin mu da mutuncin mu, kuma ya karba mana
ibadar mu. Amin.