NAFDAC ta dakatar da kamfanin ruwan roba ‘Eva Premium Table Water’

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta dakatar da aiyukkan kamfanin ruwan roba mai suna ‘Eva Premium Table Water’ dake kauyen Asejire a jihar Oyo kan rashin amincin ruwan.

NAFDAC ta sanar da wannan mataki da ta dauka ne a shafinta na Tiwita.

Mutane sun yi ta kai kukan su ga hukumar game da rashin ingancin wannan ruwa cewa zaka rika ganin datti-datti a cikin ruwan sannan wataran ma har canja kala zaka ga yana yi.

“Tabas wannan kamfanin ruwa ta yi rajista da mu kuma duk ta san sharuddan da ke kunshe a cikin takardar da suka karba.

“Wadannan sharadda kuwa sun hada da sarrafa ruwan da bashi da kala, baya wari sannan babu datti a ciki.

NAFDAC ta ce kamfanin ruwan za ta ci gaba da aiyukkantane baya hukumar ta kammala gudanar da bincike.

Hukumar ta kuma yi kira ga ‘yan kasuwan dake siyar da ruwan da wannan kamfani take sarrafawa da su daina sannan wadanda je tare da su maida wa kamfanin.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne NAFDAC ta kama kamfani dake sarrafa jabun zuma mai suna ‘Up The Rock Church of God’ a Durumi Abuja.

Shugaban hukumar Moji Adeyeye ta sanar da haka inda ta kara da cewa sun kama wannan kamfani a dalilin rashin yin rajista da hukumar da kuma yin amfani da wuri mara tsafta wajen sarrafa zuman da suke yi.

Share.

game da Author