Shugaban kungiyar Yarabawa na ‘Oodua People’s Congress’, Gani Adams ya bayyana cewa kada wani ya ce uffan idan suka dau fansar kisan ‘yar shugaban Yarabawa na Adenifere da ake zargin Fulani masu garkuwa da mutane ne suka yi a Akure.
Gani Adams ya ce sun dade suna jawo hankalin gwamnatocin yankin jihohin Yarabawa cewa fulani fa sun addabe su amma suna shiru.
” A gaskiya yanzu kam tura ta kai bango. Muna so mugayawa duniya cewa yanzu kam an kure mu duk abinda muka yi kada a zarge mu ko aga laifin mu.
” Ba wai bamu san yadda za mu tunkari abin mu kawo karshen sa bane, amma yanzu kam lallai an taba namu kuma kada wani yayi tunanin za muyi shiru ne, tabbas zamu dau fansa.
” Wannan muzgunawar yayi yawa. Zamu jira rahotan ganawan da gwamnonin mu suke yi kan tsaro a yankin. Kuma lallai a saurare mu nan ba da dadewa ba.
Daga nan sai ya jajanta wa shugaban Afenifere Rueben Fasoranti bisa wannan rashi da yayi.
Shi ma kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya muka sakon ta’aziyyar sa ga shugaban Afenifere din sannan ya umarci jami’an tsaro da su tabbata sun kami wadanda suka aikata wannan mummunar abu.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’a ne kungiyar Yarabawa na Afenifere ta sanar cewa masu garkuwa sun kashe ‘Yar shugaban kungiyar Reuben Fasoranti a hari da suka kai wa motar su.
Kakakin kungiyar Yinka Odumakin ya bayyana cewa Funke Olakunrin, mai shekaru 58 ta rasu ne bayan wasu masu garkuwa dauke da bindigogi sun bude wa motan da take ciki wuta.
Wani da abun ya faru a idonsa ya ce Fulani ne suka tare motar a hanyarsu na zuwa garin Ore daga Akure.
Sun harbi Olakunri da hakan yayi sanadiyyar rasuwarta.
Masu garkuwan sun tattare wasu motocin a wannan hari.