Jihar Zamfara ta ware hekta 300 domin gina Rugage Fulani

0

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware hekta 300 domin gina rugagen Fulania dukka mazabu uku dake jihar.

Gwamnan jihar Bello Matawalle ya sanar da haka a ziyarar da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajiamila ya kai masa a jihar.

Matawalle ya ce ” Asanina tun a da Makiyaya da manoma abokan zama ne. A wannan lokaci ne kiyayya ya fado cikin su inda har ya tsananta. Idan Aka gina rugage, za a samu natsuwa a tsakanin su da ci gaba da zaman lafiya a yankuna da dama a kasar nan sannan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa ba ma jihar Zamfara ba kawai.

Matawalle ya kuma kara da cewa gwamnati za ta gina makarantun firamare, asibitoci domin makiyaya sannan za a gina dam-dam na ruwa domin dabbobin makiyaya a wadannan rugage.

Bayan haka yayi kira ga majalisar da gwamnatin Tarayya da ta kafa wani kwamiti da zai duba halin da yankin Arewa Maso Yamma ya fada domin tallafawa yankin wajen kawo karshen ta’addanci da take fama dashi da sauran miyagun ayyuka.

Gbajiamila ya yabawa gwamna Matawalle bisa namijin kokari da ya ke yi don ganin zaman lafiya ya dawo jihar Zamfara.

“Kokarin da Bello ya yi wajen ganin an sako mutane 109 a tsakin kwanaki 10 ya nuna nasarorin da aka samu wajen kawar da aiyukkan mahara da bata gari a jihar.

Gbajiamila ya ce zai yi iya kokarin sa wajen ganin jihar ta samu duk bukatunta da gwama Matawalle ya zayyana masa jihar na bukata daga gwamnatin tarayya.

Share.

game da Author