Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta karyata bullowar cutar tarin dabobbi wato ‘Bovine tuberculosis’ a Najeriya.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu, ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Litini a Abuja.
Ihekweazu ya yi kira ga mutane da su yi watsi da wannan mangana yana mai cewa babu gaskiya a abin.
Ya ce wasu ne ke yada irin wadannan labaran karya a kafafen sada zumunta na Whatsapp da facebook a yanar gizo cewa cutar ya bullo a Najeriya. Sannan har wai shugaban kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya yi kira ga mutane da su nisanta kansu daga cin naman sa.
Ihekweazu yace domin karin bayani za a iya tuntubar su a shafinsu ta yanar gizo a www.ncdc.gov.ng, ko kuma a shafinsu na tiwita ko facebook.
A kwanakin baya ne Likitocin dabobbi a jihar Kaduna suka bayyana cewa muran dake kama dawakai da ake kira ‘Equine Influenza’ da turanci ya bullo a jihar.
Likitocin sun ga alamun haka ne a jikin wasu dawakai 18 a Zariya da Igabi inda hakan ya sa aka kebesu domin gujewa yaduwar cutar.
A wancan Kwamishinan aiyukkan gona da dabobbi Manzo Daniel ya bayyana cewa gaggauta hana yaduwar wannan cutar ya zama dole ganin cewa Igabi da Zariya ne matattarar dawakai saboda anan akafi kiwon su saboda hawan sallah da kwallon dawakai.
MENENE CUTAR TARIN DAKE KAMA DABOBBI ‘BOVINE TUBERCULOSIS’
Cutar tarin dake kama dabobbi da ake kira ‘Bovine Tuberculosis’ cuta ce dake hana dabba numfashi dakyau idan ya na dauke da cutar.
Likitocin dabobbi sun bayyana cewa cutar ta fi kama shanu ne amma sauran dabobbi kamar su akuya,rago,tunkiya,kare,mage har da ma mutum za su iya kamuwa da cutar a dalilin zama kusa da dabbar dake dauke da cutar.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da tari, mura, zazzabi da sauran su.
Likitoci sun gargadi mutane da su rika dafa nama sosai tubus kafin a ci. Sannan idan an siyo dabba a tabbata likitan dabobbi ya duba daban kafin a hadashi da sauran dabobbi a gida.
Bayan haka kuma sun bada shawara da cewa a duk lokacin da dabba ya kamu da mura a rika killace shi kadai wato a raba shi da sauran dabbobin. Sannan arika yi wa dabbobi alluran rigakafi na cututtuka.