Mai Martaba Sarkin Gwoza a Jihar Barno, Mohammed Shehu Timta, ya koma masarautar sa, bayan gudun hijirar shekaru biyar da ya shafe sakamakon mummunar harin da Boko Haram suka kai wa fadar sa.
An ruwaito yadda dandazon jama’a su ka tarbi sarkin a garin Pulka da sauran titinan garin Gwoza su ma cin cika makil da jama’a saboda murna.
Sarki Timta mai daraja ta daya a Jihar Barno, ya koma gida ne bayan samun zaman lafiya a yankin na Gwoza, wanda ya shafe shekaru da dama ya na fama da hare-haren Boko Haram.
Daga cikin masu rakiyar Sarkin Gwoza, har da Mataimakin Gwamnan Barno, Usman Kadafur, Ali Ndume wanda shi ne Sanatan Barno ta Kudu, wanda Gwoza na cikin yankin sa. Akwai ‘yan majalisar jiha da hakimai da dagatai.
Kuma an gudanar da shagulgula na al’adun gargajiya da dama a fadar sarkin.
Da ya ke wa jama’a jawabi, Gwamna Babagana Umara, wanda mataimakin sa Kadafur ya wakilta, ya bayyana cewa komawar sarkin na Gwoza gida, ya nuna cewa a yanzu doka da oda a masarautu sun sake kafuwa daram a jihar.
Daga nan ya taya sarkin komawa masarautar sa da ya yi bayan shafe shekaru biyar a Maiduguri.
Ya ce gwamnatin sa ba za ta yi wa al’ummar Gwoza rikon-sakainar-kashi ba.
Ya kuma kara jaddada cewa gwamnatin jihar Barno na ganin girma da daraja da kuma martabar sarautar gargajiya, domin ita ce ginshikin hada kan al’umma wuri daya.
“Ina kuma yin kira ga al’ummar yankin Gwoza su bai wa Sarki da jami’an tsaro hadin kai da goyon baya domin a raba yankin da fitintinun Boko Haram baki daya.
Gwamnan ya kara da alwashin cewa gwamnati za ta gaggauta karasa gyara asibitin Gwoza da gyaran hanyar samar da ruwan sha.
Sannan kuma za a gina manyan ajujuwan makarantu domin dalibai su samu damar komawa karatu da gaggawa.
Tun da farko a na sa jawabin, Sarkin Gwoza ya shaida wa jama’a cewa ya yanke shawarar komawa gida ne, domin sauran dimbin jama’ar da suka tsare su su ma su samu karfin guiwar komawa gida su ci gaba da rayuwar su a mahaifar su.
Ya kuma tuna yadda Boko Haram suka ragargaza garin tare da bayyana shi hedikwatar daular su da suka kira daular halifanci a cikin 2014.
Ya tuna cewa sakamakon mamayar da Boko Haram suka yi wa Gwoza, da dama daga cikin al’ummar garin sun arce zuwa matsugunan ’yan gudun hijira a Maiduguri, Adamawa, Abuja da Lagos. Wasu ma har a kasar Kamaru suka tsallaka gudun hijira.
Shi ma Sanata Ali Ndume ya yi kira ga mai’an tsaro da su kara karfin tsaron yankin domin kare manoma daga hare-haren Boko Haram.
Sannan kuma ya yi roko su kara karfafa mai wa Boko Haram wadanda ke kan Tsaunukan Mandara farmaki, domin a samu a kakkabe burbushin wadanda ke fitinar yankin Mandara.
Ndume ya ce idan aka kakkabe su, mazauna yankin su ma za su samu damar komawa gida.
Idan ba a manta ba, cikin Agusta, 2014, Boko Haram sun kama garin Gwoza, mai yawan al’umma 275,000. Sannan suka kaddamar da daular su a garin.
Amma daga baya sojojin Najeriya sun kwato garin.
Discussion about this post