Gwamnatin Jigawa da UNICEF sun gina dakunan bahaya 44 a jihar

0

Gwamnatin jihar Jigawa da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) sun gina dakunan bahaya 44 a karamar hukumar Birniwa.

An gina dakunan ne a babban asibitin Birniwa, makarantar sakandare na jeka ka dawo na gwamnati, makarantar sakandaren Sarkin Arewa, makarantar firamaren Matamugu, garin Kwana Dole, garin Birniwa da sauran su.

Jami’in UNICEF dake aiki a jihar Ishaku Umar ne ya sanar da haka wa manema labarai a garin Birniwa ranar Alhamis.

Umar ya ce gwamnati ta gina dakunan bahaya ne domin kawo karshen bahaya da ake yi a ko-ina a kasar nan.

Ya ce sun gina wadannan dakunan bahaya ne a tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli sannan sun haka rijiyoyin burtsatse da dama.

Umar ya kuma ce sun kafa kwamiti a kowani garin da suka gina dakunan bahaya din domin kula da gyara su.

A kwanakin baya sakamakon binciken da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya fitar ya nuna cewa mutane miliyan 47 na bahaya a waje a Najeriya.

Domin samun nasara a manufar tsaftace muhalli nan da shekara 2019 zuwa 2025 UNICEF ya ce Najeriya za ta bukaci karin dakunan miliyan biyu duk shekara na tsawon shekaru bakwai.

Jami’in UNICEF da WASH Bioye Ogunjobi ya bayyana haka a taron wayar da kan mutane game da mahimmancin tsaftace muhalli da illar yin bahaya a waje da aka yi a Abuja.

Share.

game da Author