Majalisar Dattawa ta yi kira a daina amfani da maganin ‘Avastin Injection’ a Najeriya

0

Majalisar dattawa ta umurci hukumar kula da ingancin abincin da magunguna ta kasa (NAFDAC) da ta matsa wajen dakatar da amfani da maganin allura na ‘Avastin Injection’ a kasar nan.

Majalisar ta kuma kafa kwamitin mutum bakwai da za ta hada hannu da hukumomin kiwon lafiya domin gudanar da bincike a kan wannan magani.

Majalisa ta dauki wannan mataki ne bayan sanata Aishatu Dahiru ta bayyana cewa maganin ya makantar da mutane 10 a asibitin ido na kasa dake jihar Kaduna.

Ta ce an dade ana amfani da maganin ‘Avastin Injection’ domin warkar da cututtukan da ke kama ido sannan a wani binciken da ta gudanar ta gano cewa jaridar ‘NewYork Times’ ta ruwaito cewa wannan magani na makantar da mutum.

“ A ranar 28 ga watan Mayu sama da mutane 10 sun tafi asibitin ido na kasa domin samun magani kawai sai daga neman magani sai suka makance a dalilin amfani da wannan magani.”

“A yanzu haka mutane 10 sun makance sannan wasu mutane shida basa iya gani da ido daya.

Sanata Aishatu ta ce a yanzu haka likitoci na nan na duba wadannan mutane sannan babu tabbacin ko idon su zai dawo kamar yadda yake a da.

Ta yi kira ga gwamnati ta ta matsa kaimi a daina shigo wa da wannan magani.

Share.

game da Author