Majalisar ta ce lalle ya kamata a kara ware wa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko kudade a cikin kasaffin kudin kasa domin samun inganci a aikin su.
Majalisar ta yi wannan kira ne bayan kokawan da sanata Oluremi Tinubu ta yi kan cewa rashin warewa cibiyoyin kiwon lafiya isassun kudade na daga cikin matsalolin dake hana mutanen kasar nan samun kiwon lafiya na gari.
Ta ce a yanzu haka cibiyoyin kiwon lafiya kashi 20 bisa 100 daga cikin 30,000 ne ke aiki a kasar nan.
Sannan matsalolin da ya hada da rashin ma’aikata, rashin magunguna da sauran kayan aiki ya mamaye kashi 20 din dake aiki.
“ An kafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a kasar nan a 1998 domin tallafa wa talakawa amma sai gashi yau an wayi gari wadannan asibitoci basu aiki yadda ya kamata inda dole talaka ke garzayawa manya-manyan asibitoci domin neman magani.
A zauren sanatoci 108 ne suka mara wa sanata Tinubu baya.
Sannan sanatoci kamar su Chimaroke Nnamani, Alero Adamu da Dahiru Aishatu sun yi kira ga gwamnati da ta karkato da hankalinta wajen ganin cewa mutanen kasar nan sun sami kiwon lafiya na gari a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.
Sun kuma yi kira ga ma’aikatar muhalli da ta kirkiro dokoki da za su tilasta wa ma’aikatu a kasar nan shiga shirin tsarin inshoran kiwon lafiya.
Discussion about this post