Gwamna Bagudu na jihar Kebbi ya sauke shugabanin kananan hukumomin jihar

0

Mai taimakawa gwamnan jihar Kebbi kan harkokin yada labarai, Abubakar Dakingari ya sanar da cewa gwamna Bagudu ya sauke duka shugabannnin kananan hukumomin jihar su 21.

Dakingari yace gwamnati ta sauke shugabanin da kansilolin su ne ganin cewa wa’adin aikin su duk ya cika daga yau Laraba 24 ga watan Yuli.

Ya ce gwamnati ta kuma umurce su da su mika takardun aiki na kowacce karamar hukuma ga babban sakataren karamar hukumar.

Wasikar babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi da ayyukan masarautu na jihar ya bayyana cewa dama an zabe su ne tun a shekarar 2017 da hakan ya sa a sauke su yanzu.

A karshe ya yabawa shugabannin kananan hukumomin bisa hidima da suka yi wa kanan hukumomin su na aiki tukuru domin ci gaban al’umman su.

Share.

game da Author