Cif Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya bayyana cewa wasu fitinannun gara da zago ne suka cinye masa takardar shaidar kammala karatun firamare din sa.
Muhammad ya ce gara da zago sun shiga dakin da ya ke ajeye shirgin takardun sa, a gidan sa na Bauchi a cikin 1998, inda suka durfafi dukkan takardun sa, sai da suka cinye su karkaf.
Ya ce cikin kayan sa da aka cinye har da satifikef din sa na kammala firamare.
“Sun cinye komai, ba su bar ko da wata guntuwar takarda ba.”
Haka ya rubuta a cikin wata rantsuwar-kaffarar-kwansitushin da ya aika wa Majalisar Dattawa domin neman amincewa a nadin da Buhari ya yi masa.
Wannan kwafen takardar rantsuwa dai ta rika yawo a soshiyal midiya tun daga shekaranjiya Litinin. Amma PREMIUM TIMES ba ta yi saurin bugawa ba, har sai da ta kara zakulo wasu karashen kwafe-kwafe na takardun bayanan Cif Jojin da ya aika majalisa saboda neman a tabbatar da shi Cif Joji.
Tanko ya yi ‘rantsuwar kaffara’ a ranar 13 Ga Fabrairu, 2002, a lokacin ya na mai shari’a a Kotun Daukaka Kara ta Jos, Jihar Filato. Ya zama Mai Shari’a a Kotun Koli cikin 2007.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Cif Jojin Tarayya, bayan ya cire Cif Joji Walter Onnoghen daf da zaben 2019.
Jim kadan bayan nada shi, sai sai wani lauya ya shigar da karar zargin sa da kantara karyar rage yawan shekaru haihuwar sa.
An yi zargin cewa ya rage shekara uku, daga 31 Ga Disamba, 1950, zuwa 31 Ga Disamba, 1953.
Muhammad Tanko dai ya karyata wannan zargi. Shi kuma lauyan da ya maka shi kotu, aka kori karyar tare da cin shi tarar naira milyan 10.
Mai Shari’a ya ce lauyan ba shi da ikon shigar da waccan kara, kuma ba ta ma da wani tushe ballantana hurumi.
Sai dai Premium Times ba ta sani ba a zuwa yanzu shin an biya tarar, ko kuwa daukaka karar a ka yi.
Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne Majalisar Dattawa ta amince da nadin Tanko Muhammad.
Sai dai kuma babban mai shari’ar na ci gaba da shan habaici da yamadidi a soshiyal midaya.
Hakan ya biyo bayan kasa bayar da cikakkiyar amsa da ya yi a kan tambayar da aka yi masa dangane da wani baubawan-burmin hukunci da Kotun Koli ta yanke a shari’ar zaben gwamnan jihar Osun.