A bincike da kungiyar kiwon lafiya ta duniya bayyana cewa an cewa a maganin ‘Dolutrgravir (DTG) ya fi maganin ‘Efavirenz (EFV) inganci wajen kawar da cutar Kanjamau a jikin wanda ya kamu.
WHO ta ce haka ya biyo bayan bincike ne da aka yi game da ingancin wadannan magunguna.
Kungiyar ta bayyana cewa a shekarun baya da aka fara sarrafa wannan maganin maganin DTG na cutar da lafiyar jaririn dake cikin mahaifiyarsa domin maganin kan sa a haifi jarirai dake da nakasu a jiki.
A dalilin wannan sakamako ne WHO ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su hana mata masu ciki dake dauke da Kanjamau yin amfani da DTG cewa maganin EFV ya fi dacewa.
Daga cikin kasashen duniya 18 da WHO ta gudanar da bincike, kasashe 12 na fama da matsalolin rashin aikin maganin.
A dalilin haka WHO ta gudanar da bincike domin gano hanyar da zai fi dacewa wajen kawar da wannan matsalar.
Yayin da suke gudanar da bincike a kan maganin DTG sai suka gano cewa maganin DTG baya cutar da kiwon lafiyar jariran dake cikin mahaifan su sannan DTG na kawar da matsalolin rashi aikin magani a jikin mai dauke da Kanjamau.
Hakan na nuna cewa mace mai ciki kuma tana dauke da cutar za ta iya amfani da wannan magani batare da ya cutar da lafiyar dan dake cikinta ba.
Sannan matsalolin da akan samu a dalilin amfani da magunguna kamar su amai, rashin iya barci, yawan jin gajiya a jiki da makamantan su na DTG ba kai na sauran magungunan da ake amfani da su ba.
A karshe WHO ta saka wannan magani a cikin jarin ingantattun magungunan kawar da cututtuka domin gwamnatocin duniya su rigaka amfani da shi.
Discussion about this post