FIFA ta yi wa Najeriya tayin daukar nauyin Gasar Kofin Mata ‘Yan Kasa Da Shekaru 20 Na Duniya

0

Shekaru 10 kenan rabon da Najeriya ta karbi bakuncin gasar kwallo ta duniya, sai ga shi kuma a yanzu Hukumar Shiryya Gasar Kwallon Kafa ta Diniya, FIFA ta yi wa Najeriya tayin daukar nauyin Gasar Kwallon Kafa ta Mata ‘Yan Kasa Da Shekara 20 ta duniya.

Majiya daga Hedikwatar FIFA a birnin Zurich, ta gulmata wa PREMIUM TIMES cewa Kungiyar Kwallon Kafa ta Najeriya na nan na matsa-lambar ganin cewa FIFA ta amince domin a buga wannan kasaitacciyar gasar kwallon kafa ta mata a Najeriya.

Tuni wannan majiya ta kara da cewa FIFA na nan na shirye-shiryen turo tawagar gani-da-ido, wadda za ta duba ko Najeriya ta cancanci karbar bakuncin shirya gasar.

Tawagar wadda aka ce za ta shafe kwanaki hudu ta na duba wurare a Najeriya, za ta duba filayen kwallon da suka cancanta, asibitoci da kuma batun da ya shafi tsaro.

An kuma tabbatar da cewa FIFA za ta kashe dala milyan 4 a wajen gasar. Hakan ya nuna cewa Najeriya ba za ta yarfe gumin kwasar kudade ta na kashewa a kan gasar sosai ba.

Cikin shekara 2002 ne aka fara gasar mata matasa na duniya ‘yan kasa da shekaru 19.

Anma daga baya sai aka maida shi na ‘yan kasa da shekaru 20.

Share.

game da Author