Yayin da ake ci gaba da nuna damuwa dangane da yadda shanu ke karakainar kiwo a Abuja, Hukumar Kula Da Kare Muhalli ta Babban Birnin Tarayya, AEDP ta bayyana cewa babu inda wata rubutacciyar dokar kasar nan ta haramta gilmawar shanu a cikin Abuja.
Yayin da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES a ofishin sa a cikin wannan makon, Kakakin Yada Labarai na AEDP, Muktar Ibrahim, ya yarda da cewa Misitan da ya sauka kwanan baya ya haramta kiwon shanu a cikin Abuja.
Sai dai kuma ya kara da cewa ministan ya yi furucin ne kawai da baki, amma babu inda aka rattaba dokar a rubuce.
“Ko da an rattaba ta ma, to ta ci karo da dokar da ta kafa Hukumar AEDP kenan.”
Idan ba a manta ba, a lokacin da aka kafa AEDP cikin 2016, sai da minista Mohammed Bello na Abuja ya zauna da Kungiyar Miyetti Allah, inda ya nemi su kawo Fulani matasa masu ilmi domin a saka su aiki a kwamitin hukumar.
“Ku fahimta cewa an hana kiwon shanu cikin Abuja ba don komai ba sai saboda tsaron lafiyar shanun ku da kuma rayukan jama'”.Haka Bello ya shaida musu a lokacin.
Daga nan ya ce tilas makiyaya su daina shigowa cikin labobi da koramun cikin Abuja su na kiwo.
Ya kuma kafa kwamiti a karkashin Abdullahi Morjel domin korar makiyaya daga cikin Abuja.
Shekara uku bayan wannan, a yanzu kuma makiyaya sun dawo kiwo cikin Abuja.
Kakakin AEDP ya shaida wa wakilinmu cewa doka dai abin da ta hana a Abuja shi ne yawon dabbobi su kadai ba tare da kowa mai kula da su ba.
A kan haka ne ya ce kwanan nan za su dawo da kamen shanun da aka gani su na karakaina a Abuja.